Amarya Ta Sharbi Kuka A Wajen Baikonta Yayin da Mahaifiyarta Ta Kawo Mai Daukar Hoton Kauye, N10,000 Ya Karba

Amarya Ta Sharbi Kuka A Wajen Baikonta Yayin da Mahaifiyarta Ta Kawo Mai Daukar Hoton Kauye, N10,000 Ya Karba

  • Wata amarya yar Najeriya ta fusata a yayin baikon aurenta saboda mai daukar hoton da yayi aiki a taron
  • Bikin ya gudana ne a yankin Offa, kuma ta baiwa mahaifiyarta ragamar kawo mai daukar hoto mai kyau wanda ke cajan N55,000
  • Sai dai kuma, mahaifiyarta ta sauya mai daukar hoton sannan ta nemo mai saukin kudi wanda ya cajeta N10,000 amma bai yi aiki mai kyau ba

Kwara - Wata kyayyawar amarya yar Najeriya ta fusata sosai a yayin baikon aurenta a yankin Offa da ke jihar Kwara.

Budurwar mai suna Aisha Odunola a Twitter, ta ce mahaifiyarta ta dauka mai hoto wanda sam bai kware ba don yin aiki a wajen taron.

Amarya
Amarya Ta Sharbi Kuka A Wajen Baikonta Yayin da Mahaifiyarta Ta Kawo Mai Daukar Hoton Kauye, N10,000 Ya Karba Hoto: @aishatodunola.
Asali: Twitter

Kyakkyawar amaryar ta yo hayar wani kwararren mai daukar hoto sannan ta bukaci mahaifiyar tata ta tawo dashi idan za ta zo.

Kara karanta wannan

Tashi Ka Nemi Abun Yi: Fusatattar Matar Aure Ta Dangwararwa Da Miji Kwano Babu Abinci

Kwararren mai hoton ya caji N55,000, wanda a cewar mahaifiyar tata yayi tsada da yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahaifiyar tata ta sallame shi sannan ta nemo wanda da ya yarda zai yi aikin kan N10,000 amma daga bisani ya bukaci N15,000.

Aisha ta zub da hawaye a ranar baikonta

Aisha ta sha kuka saboda mai daukar hoton kuma sai da aka roketa kan ta bari taron ya ci gaba kamar yadda aka tsara.

Ta fada ma Legit.ng cewa sabanin ita, sam lamarin ba dami mijinta ba.

Matashiyar ta wallafa wasu daga cikin hotunan da mai daukar hoton kauyen da mahaifiyarta ta kawo ya dauka.

Ta ce:

“Maza gaba daya duk wadannan lamuran na hoto bai damesu ba, ya sha mamaki wai ina kuka wiwi saboda mai daukar hoto kuma bayan ya rokeni na tsawon lokaci, sai muka je muka hadu da yan uwansa a wajen taron don mun rigada mun yi katti kuma suna ta kira.”

Kara karanta wannan

Ni Kadai Iyayena suka Haifa: Matar da ke da Tattaba Kunne 101 ta Bayyana Hotunansu

Kalli wallafarta a kasa:

Legit.ng ta zanta da wani mai daukar hoton zamani, Abdul Graphics don jin ta bakinsa kan yadda suke fama da abokan harka inda yace suna aiki ne iya kudinka iya shagalinka.

Ya ce:

“Mutane basu gane ba daukar hoto suna ya tara, domin akwai hoton da ya amsa sunansa hoto kamar kayi magana na ciki ya amsa akwai kuma muna hoto. Ba kowani mutum ne yake iya sakin bakin aljihu don ayi masa aiki mai kyau ba.
“Duk wanda ya siya rariya ya zan zata zub da ruwa ai daga jin kudin da suka biya na wannan hoton ka san baza ayi abun kirki ba. Ni yanzu mafi karancin kudin da nake chaja idan dai kana son nayi maka aiki mai kyau shine N40,000 a kwana daya. Toh ko kamarar ai iri-iri ce.”

A Shirye Nake Idan Na Samu Miji Zan Yi Aure: Tsohuwa Mai Shekaru 70 Tace Tana Neman Saurayi

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Aka Yi Mata Kwalkwabo Bayan Mutuwar Mijinta, Bidiyon Ya Taba Zukata

A wani labarin, Alphonsine Tawara ta bayyana cewa har yanzu bata da saurayi kuma ita din budurwa ce sabuwa dal a leda duk da kasancewar ta yi shekaru 70 a duniya.

Matar, wacce ta fito daga kasar Kongo, ta bayyana cewa ta sadaukar da rayuwarta don ceto kannenta sannan cewa za ta yi aure idan ta samu miji.

Alphonsine ta ce ta tsaya har dukka kannenta su kammala karatu amma bata taki sa’a ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng