Gwamnatin Najeriya Ta Umarci Shugabannin Jami’a Su Bude Jami’o’i, Dalibai Su Koma Karatu
- Gwamnatin Najeriya ta ce ba zai yiwu dalibai su ci gaba da zaman banza ba, dole ASUU su koma bakin aiki
- Tuni aka ba da umarni ga shugabannin jami'a da su gaggauta kiran malamai da dalibai kowa ya koma makaranta
- ASUU na yajin aiki tun watan Fabrairun bana, ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin kungiyar da gwamnati
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da jami'o'i (NUC) ta umarci shugabannin jami'a da su gaggauta bude makarantu kana dalibai su koma karatu.
Wannan na fitowa ne daga wata wasikar da ke dauke da sa hannun daraktan kudi na NUC, Sam Onazi a madadin babban sakataren hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed.
Jaridar Punch ta ce ta samu wasikar ne kai tsaye daga hukumar, inda aka umarci shuganannin jami'o'i da masu gudanar dasu da su koma bakin aiki.
Wasikar ta ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ku tabbata mambobin ASUU sun koma bakin aiki nan take; a koma harkokin yau da kullum da ayyukan jami'a na yau da kullum a dukkan jami'o'i."
Yadda batun yajin ASUU yake
Idan baku manta ba, kotun masana'antu ta kasa a ranar Labarar da ta gabata ta umarci mambobin ASUU da su gaggauta janye yajin aiki, lamarin da ya jawo cece-kuce a Najeriya.
ASUU ta fara yajin aiki ne tun ranar 14 ga watan Satumba bisa rashin samun abubuwan da take bukata daga hannun gwamnati, haka nan Punch ta ruwaito.
An sha ganawa tsakanin ASUU da jami'ai da hukumomin gwamnati, amma lamarin ya ki kai wa ga mafita mai dorewa.
Bayan gaza shawo kan ASUU ne gwamnatin Najeriya ta maka kungiyar kotu.
Gwamnati ta nemi kotu ta tursasa malaman jami'a su koma bakin aiki, kana a hana su daukar wani sabon matakin shiga yajin aiki a nan gaba.
Bayan nazari, kotu ta umarci ASUU ta koma bakin aiki, amma hakan bai yiwuwa ba.
Tuni kungiyar ta dage kara, ta kuma kawo batutuwa 14 da take so a baje kolinsu a kotun daukaka kara.
Dalibai Sun Tubure Bayan da Aka Umarci Kungiyar ASUU Ta Koma Bakin Aiki
A wani labarin, kungiyar daliban Najeriya ta kasa (NANS) ta yi watsi da hukuncin kotu na umartar kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta koma bakin aiki, rahotom jaridar Punch.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta kungiyar, Giwa Yisa Temitope ta ce, sam wannan kira ba komau bane face yanke hukunci kan rashin adalci da daidaito.
Hakazalika, kungiyar ta ce tun farko ma bai kamata gwamnati ta maka kungiyar malamansu a kotun ma'aikata ba.
Asali: Legit.ng