Yan Bindiga Sun Kashe Bayin Allah, Sun Sace Mata Masu Shayarwa da Jarirai a Zamfara
- Miyagun 'yan bindiga sun kai sabon mummunan hari kan bayin Allah a garin Tauji dake karamar hukumar Maru a Zamfara
- Bayanai sun yi nuni cewa mutum uku sun rasa rayuwarsu yayin da maharan suka sace mata masu shayarwa guda Takwas
- Wannan na zuwa ne a lokacin da Sojoji ke ci gaba da kai samame maɓoyar 'yan ta'adda a sassan jihar
Zamfara - Aƙalla mutum uku suka rasa rayukansu kuma aka sace mata masu shayarwa Takwas yayin da wasu yan bindiga suka kai hari yankin Tauji, Kanoma ta arewa, ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Wani ɗan asalin yankin, Muhammad Maisa, wanda ya zanta da jaridar Punch, yace lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:40 na dare lokacin da wasu sanannun 'yan bindiga suka shigo yankin.
Maisa ya bayyana cewa da zuwan 'yan bindigan a kan Babura ba wata-wata suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin su tsoratar da mutane.
Mutumin yace:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Daga nan sai suka riƙa kutsawa gida-gida suna neman mutanen da zasu yi garkuwa da su. Sun yi nasarar tafiya da matan aure Takwas, ma fi yawansu suna shayarwa, sannan kuma suka kashe mutum uku da suka yi yunkurin tsere wa."
Basaraken garin, Alhaji Ibrahim Nabature (Sarkin Sudan) ya tabbatar da kai sabon harin. Ya yi kira ga gwamnatin Zamfara ta ƙara girke jami'an tsaro a yankin don kare hare-haren yan ta'adda.
Duk wani yunkuri domin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda reshen Zamfara, Muhammad Shehu, bai kai ga nasara ba domin lambarsa ba ta shiga sam.
Zamfara na ɗaya daga cikin johohin da ke fama da ayyukan ta'addancin 'yan bindiga a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wani haifaffen garin da abun ya faru ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa abin da ya faru ba sabon abu bane a yankin Maru, jihar Zamfara ya saba faruwa lokaci bayan lokaci.
Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda hali na tsaro, ya faɗa mana cewa maharan sun ƙashe mutum uku, ciki har da ɗalibinsa na Sakandire.
Yace:
"Sun zo da ƙarfe ɗaya na dare suka ƙashe mutum uku, Zubairu Akinbo, Awwal Junaidu da ake kira ɗan Abuja da Aminu Ahmad, wanda ya kasance ɗalibina a makaranta."
"Sai mata 8 da suka ɗauka, wasu daga cikinsu suna goyo amma duk an tafi da su jeji kuma har yanzu babu labari."
Bugu da ƙari, Mutumin yace yan ta'adda sun sake shiga ƙauyen Kanoma (Zanau) ranar Litinin 26 ga wata, inda suka yi awon gaba da wani mutumi, Badamasi Umar, a gonarsa.
Bello Turji ya gargaɗi gwamnati
A wani labarin kuma Kasurgumin Dan Bindiga, Bello Turji, Ya Maida Martani Kan Harin da Jirgin Sojin Najeriya Ya Kai Gidansa a Zamfara
Sanannen ɗan bindigan nan, Bello Turji, ya nuna damuwarsa bisa harin da jirgin sojoji ya kai gidansa a Zamfara.
Turji yace harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutanensa da dama duk da ya tuba ya rungumi zaman lafiya tsawon watanni.
Asali: Legit.ng