Labaarin Wani Dan Saudiyya Ya Yi Ikirarin Cewa Ya Yi Aure Sau 53 a Cikin Shekaru 43

Labaarin Wani Dan Saudiyya Ya Yi Ikirarin Cewa Ya Yi Aure Sau 53 a Cikin Shekaru 43

  • Domin nemawa kansa zaman lafiya da kwanciyar hankali, wani balaraben Saudiyya ya ce aure sau 53 ya yi a cikin shekaru 43
  • Mutumin mai shekaru 63 ya bayyana sirrin yin wadannan aure-aure, ya kuma bayyana halin da yake ciki
  • Ya auri mata da yawa 'yan kasar Saudiyya, amma ya auri wasu a kasashen da ya yi tafiyar kasuwanci a duniya

A kokarinsa na neman kwanciyar hankali da dadin rai, wani balarabe ya fadi tarihin rayuwarsa, ya ce mata 53 ya aura a cikin shekaru 43 kacal.

Abu Abdullah ya ce ya yi aurensa na farko ne a lokacin yana da shekaru 20, kuma matar da ya aura ta girme shi da shekaru shida.

Mutumin da ya yi aure sau 53 don ya samu kwanciyar hankali
Labaarin Wani Dan Saudiyya Ya Yi Ikirarin Cewa Ya Yi Aure Sau 53 a Cikin Shekaru 43
Asali: UGC

An kakaba masa “Polygamist of the century”, wato mutumin da ya fi yawan aure-aure a wannan kanin saboda yawan auren da ya yi, kamar yadda MBC ta bayyana.

Kara karanta wannan

Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe

Ya shaidawa kafar labarai mallakin Saudiyya cewa, aure mafi gajeren zango a rayuwarsa ya mutu ne a dare daya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"A lokacin da na yi auren fari, ban shirya auren mace fiye da daya ba saboda na samu kwanciyar hankali ga kuma 'ya'ya.
"Amma bayan wani dan lokaci, sao matsaloli suka dumfaro sai na yanke shawarin kara aure a lokacin shekaru na 23 kuma na shaidawa matata shawarin da na yanke."

A cewarsa, shawarin nasa dai bai warware matsalarsa ta neman matar da za ta saka shi farin ciki ba.

Ya yi alkawarin ba zai sake aure ba

A cewar rahoton Gulf News, Abdullah matsalolin sun kara tunbatsa tsakanin matansa biyu, don haka ya yanke shawarin auren wasu mata biyu, daga nan kuma ya daga ma biyun da ke ba shi ciwon kai jan kati.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jigon APC a Arewa ya tada kura a Twitter, ya ce ya ga sarauniyar Ingila a aljanna

Ya ce a hakan fa yana yi musu adalci a tsakaninsu, kuma daga aure-auren da ya yi, da yawan matan 'yan kasar Saudiyya ne, amma ya auri 'yan wasu kasashen daban.

Abdullah ya ce ya yi aure a kasashen waje domin kare kansa a tafiye-tafiyen da ya yi a kasashen duniya na tsawon watanni uku zuwa hudu.

A cewarsa:

"Kowane namiji a duniya na da burin zama da mata daya har kashen rayuwarsa....Kwanciyar hankali ba ta samuwa daga mace mai kananan shekaru, amma ana samu a mai shekaru d ayawa.

Duk da tarihin da ya kafa, ya zuwa yanzu dai matarsa daya yake tare da ita, kuma ya ce bai da niyyar kari a nan gaba.

Yadda Budurwa Ta Hada Shagalin Murnar Haihuwarta, Amma Kawayenta Suka Yi Zuwa

A wani labarin, wata matashiya mai shekaru 18 ta zaman zugum yayin da ta yi bikin cika shekara amma babu wanda ya hallara.

Kara karanta wannan

Akwai yunwa a kasar nan: Yadda matashi ya lamushe malmala 10 na tuwo cikin mintuna 10

Mutane da dama sun nuna kauna da taya ta shagalai ganin yadda aka kowa ya guji zuwa wurin wannan shagali.

Wata mata da tace 'yar uwar budurwa mai shagalin ne ta yada bidiyo a TikTok, ta nuna yadda dakin shagalin ya kasance babu kowa a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.