A Baya Ta Mallaki Motoci Da Gidaje Amma Yanzu Ta Talauce Tana Bara: Labarin Wata Milloniya

A Baya Ta Mallaki Motoci Da Gidaje Amma Yanzu Ta Talauce Tana Bara: Labarin Wata Milloniya

  • Wata Mata mai suna Dorcas Kagendo wacce ta kasance Milinoya mai kudi amma daga baya aka ganta a titi tana bara
  • Dorcas ta zama Miloniya tun tana yar shekara 33 kuma ta mallaki motoci da gida kafin iftila'i ya fada mata shekaru biyu da suka gabata
  • Bayan talaucewar da tayi, yanzu tana fama da cututtuka daban-daban dale gab da hallaka rayuwarta

Dorcas Kagendo, wata 'yar shekar 50 wacce ta kasance attajira tana kira ga jama'a su kawo mata dauki.

Matar yar kasar Kenya ta kasance mai kudi lokacin tana matashiya amma abubuwa suka sauya daga baya.

Photo Credit: YouTube/Afrimax
A Baya Ta Mallaki Motoci Da Gidaje Amma Yanzu Ta Talauce Tana Bara: Labarin Wata Milloniya Hoto: YouTube/Afrimax
Asali: UGC

Labarinta

Tashar Afrimax ta yi hira da Dorcas wacce aka gani a titi tana bara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta ce bayan kammala karatu, ta samu aikin sakatare daga baya kuma ta zama jagora.

Kara karanta wannan

Da Gaske Akwai Maganar Aure Tsakanin Darakta Mustapha Waye Da Hajara Izzar So Kafin Rasuwarsa? Jarumar Ta Fayyace Gaskiyar Lamari

Daga nan ta fara samun kudi inda ta sayi manyan motoci, gidaje da kadarori. Hakazalika tayi aure amma Mijin ya tafi daga baya.

An nuna hotunan motocin da ta siya lokacin da take cin gari.

Dorcas tace rayuwarta ta fara samun matsala ne lokacin da ta samu wani aiki a kasar Saudiyya.

Ba da dadewa ba ta fara fama da ciwon koda, ciwon siga, ciwon huhu, da kansa. Sakamakon haka aka koreta daga Saudiyya.

Tace ta koma gida Kenya inda ta fara sayar da dukiyoyinta don jinya, har komai ya kare.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel