Kungiyar Musulunci, MURIC, Ta Yi Martani Kan Haramta Saka 'Mini Skirt' A Makarantun Jihar Abia

Kungiyar Musulunci, MURIC, Ta Yi Martani Kan Haramta Saka 'Mini Skirt' A Makarantun Jihar Abia

  • Kungiyar musulunci ta MURIC ta jinjinawa gwamnan Jihar Abia, Farfesa Charles Soludo kan haramta saka gejeren sket a makarantu
  • MURIC ta ce wannan matakin da Soludo ya dauka ya dace da kiraye-kirayen da kungiyoyin musulmi suka dade suna yi na nema wa mata yancin saka hijabi don suturta jikinsu
  • Farfesa Akintola Ishaq, shugaban MURIC na kasa ya yi kira ga sauran gwamnonin Najeriya su yi koyi da wannan matakin da Solodu ya dauka na kare mutuncin yara mata

Kungiyar musulunci ta MURIC ta yaba wa Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra kan haramta saka gajerun sket wato 'mini skirt' a makarantun mata na gwamnati da masu zaman kansu a jihar.

MURIC ta ce haramtawar ya yi daidai da neman yancin saka hijabi da kungiyoyin musulmi ke yi a Najeriya, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe

Farfesa Akintola
Kungiyar Musulunci, MURIC, Ta Yi Martani Kan Haramta Saka 'Mini Skirt' A Makarantun Jihar Abia. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Twitter

Kungiyar, cikin sanarwar da shugabanta, Farfesa Ishaq Akintola ya fitar ta ce matakin da Gwamna Soludo ya dauka kishin kasa ne da hangen nesa da ya dace sauran gwamnoni su yi koyi da shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani sashi cikin sanarwar:

"Wannan daya daga cikin hanyoyin gane uban kasa ne a maimakon gama-garin yan siyasa wadanda zabe na gaba ne kawai ke gabansu. Iyayen kasa suna tunanin kasa ne yayin da yan siyasa zabe na gaba suke tunani. Charles Soludo ya nuna shi uban kasa ne ya zabi kare mutuncin ya mace da tarbiya da ladabi.
"Ya kamata sauran gwamnoni su yi koyi da shi. Babu shakka wasu unifom din makarantu a yanzu suna iya janyo sha'awa. Hatsari ne ga yara mata. Dole mu kare yaya mata daga idanun maza wadanda ba su kiyaye abin da suke kallo."

Kara karanta wannan

Ana Samun Rabuwar Kai a Kamfe Saboda Tinubu Ya Jawo Gwamna, Ya Ba Shi Mukami

MURIC ta yi kira ga sauran gwamnonin Najeriya su yi koyi da Soludo

Akintola ya kara da cewa wannan matakin na Soludo ya wanke kungiyoyin musulunci da suka dade suna kira ga cewa a rika saka hijabi.

An Haramta Amfani Da 'Mini Skirt' A Matsayin Unifom A Makarantun Wata Jihar Kudancin Najeriya

Tunda farko, Gwamnatin Jihar Anambra ta haramta saka gajerun siket wato 'mini skirt' a matsayin unifom a dukkan makarantun jihar, Premium Times ta rahoto.

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Farfesa Ngozi Chuma-Udeh, ne ta bayyana hakan a Awka a ranar Lahadi tana mai cewa sanarwar haramcin ya zama dole domin makarantu za su dawo hutu a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164