Lafiyar Nnamdi Kanu Ta Kara Tabarbarewa, Yana Fama da Ciwon Hanji, Inji Lauyansa
- Yayin da hukumomin Najeriya ke ci gaba da tsare Nnamdi Kanu bisa tuhumarsa da cin amanar kasa, an ce yana fama da ciwo
- Lauyansa ya fitar da wata sanarwar dake bayyana halin da yake ciki, inda yace DSS ta hana shi neman magani
- An kamo Nnamdi Kanu daga kasar waje, an gurfanar dashi a gaban kotu watanni 14 da suka gabata
Najeriya - Yanzu muke samun labarin cewa, lafiyar shugaban 'yan awaren Biafra, Nnamdi Kanu ta tabarbare sakamakon ci gaba da ajiye shi da aka yi a hannun hukumomin Najeriya.
Lauyansa, Ifeanyi Ejiofor ya bayyana cewa, Kanu na fama da cututtuka da dama da suka shafi ciki, ciki har da kuna da yake fama da ita mai kama da cutar olsa.
Lauyan nasa ya bayyana hakan ne a yau Litinin 19 ga watan Satumba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Idan baku manta ba, Nnamdi Kanu ya kasance a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) na tsawon watanni 14 kenan, inda yake fuskantar shari'a da gwamnati bisa zarginsa da cin amanar kasa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ejiofor ya bayyana cewa, ya ziyarci Kanu a magarkamar DSS, kuma tabbas ya same shi cikin yanayin dake bukatar taimako.
Ya bayyana cewa, akwai bukatar DSS ta fahimci cewa, ba ita ce mai kirkirar doka ba, don haka ya kamata ta bi umarnin kotu na sassautawa Kanu.
Ya bayyana cewa:
"A halin yanzu, Onyendu na fuskantar ciwon hanji dake bukatar shan magungunan da zai sa radadi ya lafa, saboda tsananin kuna da yake ji kirji. Abin bakin ciki, hukumar DSS ta hana a samar masa maganin rage radadi da zai sa ciwon ya lafa."
Ya ce, a halin yanzu dai suna kokarin yadda za a yi a samarwa Nnamdi Kanu hakkin neman lafiya kamar yadda doka ta tanada, Politics Nigeria ta ruwaito.
Ba mu da hannu a kama Nnamdi Kanu, gwamnatin kasar Kenya ta fadawa kotu
A wani labarin, gwamnatin kasar Kenya ta kara nisanta kan ta daga kama shugaban haramtaciyyar kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra ta IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, rahoton Vanguard.
Gwamnatin yayin kare kan ta a kotun da dan uwan Kanu, Kingsley Kanunta Kanu ya shigar da kara a maimakon shugaban IPOB din, gwamnatin kasar Kenya ta ce ba da izinin hukuma gwamnati ta kama Kanu ba.
Takardar da lauyan Kanu na musamman, Aloy Ejimakor ya gabatar wa Vanguard a maimakon dan’uwan Kanu ta nuna bayan zaman kotun ranar 2 ga watan Nuwamba ta nuna hakan.
Asali: Legit.ng