Dan Gwamnan Gombe, Misbahu Ya Angwance Da Kyayyawar Amaryarsa Ameera Babayo
- Jihar Gombe ta yi cikar kwari a karshen makon jiya yayin da Gwamna Inuwa Yahaya ya aurara da dansa, Misbahu
- Misbahu ya auri sahibarsa Ameera Babayo a wani kasaitaccen biki da ya samu halartan manyan masu fada aji a kasar nan
- Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima na cikin wadanda suka halarci daurin auren
Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya karbi bakuncin manyan mutane daga fadin kasar yayin da ya aurar da dansa, Misbahu Yahaya.
Misbahu ya angwance da kyakkyawar amaryarsa mai suna Amina (Ameera) Babayo, jaridar Thisday ta rahoto.
Babban limamin masallacin Juma’a na Gombe, Sheikh Ali Hammari, ne ya jagoranci daurin auren Misbahu da Amina a karshen makon jiya.
Mai martaba sarkin Gombe, Dr. Abubakar Shehu Abubakar III, ne ya tsaya a matsayin wakilin ango, yayin da Alhaji Kawu Adamu yayi wakilin amarya,
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Waliyin amarya ya bayar da auren Ameera ga Misbahu ta hannun wakilinsa wanda ya samu wakilcin babban hakimin Gombe, Alhaji AbdulKadir Abubakar Umar, kan sadaki N100,000.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a wajen daurin auren.
Sauran manyan da suka halarci daurin auren sun hada da dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Ahmed Tinubu; abokin takararsa, Kashim Shettima; shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu.
Gwamnonin da suka hallara sun hada Dr Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno.
Sai Gwamna Abdulkadir Bala Mohammed na jihar Bauchi, Gwamna mai Mala Bunin a Yobe, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da sauransu.
Hakazaika, daurin auren ya samu halartan manyan yan kasuwa, manyan yan siyasa, manyan lamai, sarakunan gargajiya, abokai, hadimai da yan uwan ango da amarya.
Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna jin dadi da irin kaunar da aka nuna masa na halartan wannan babban taro na aurar da dansa. Ya kuma yi godiya ga duk wadanda suka hallara cewa zuwan nasu ya kara kayatar da bikin.
Bidiyo: Budurwar Da Ta Rabu Da Saurayinta Talaka Saboda Mai Kudi Ta Koka, Bata Auru Ba Bayan Shekaru 10
A wani labarin, wani bidiyo mai tsawon sakanni 56 a TikTok ya nuno wata matashiyar budurwa wacce tace shekarunta 40 amma har yanzu bata da aure.
A cewar budurwar, wani saurayi mai dattako ya nemi aurenta shekaru 10 da suka gabata amma sai daga bisani ta soke shirye-shiryen auren ana saura sati biyu.
Ta tuna yadda ta soke auren saboda ta samu wani saurayi mai kudi wanda take tunanin zai aure ta.
Asali: Legit.ng