Shekaru 22 Ina Bai wa Najeriya Gudumawa Babu Sakamako, Tsoho Mai Shekaru 72
- Farfesa Adebowale ya bayyana takaicinsa kan yadda ya dinga hidimtawa Najeriya amma har yanzu babu sannu bare nagode daga Buhari
- Farfesan ya sanar da yadda ya zama jigon bayar da shawari a fannin tsarikan tattalin arzikin kasar nan amma shiru kake ji
- Ya bukaci Buhari da ya tumbuke Osinbajo daga shugabancin kwamitin farfado da tattalin arziki tare da nada shi a wurin
Tsoho mai shekaru 72 kuma malamin makaranta, Farfesa Mufutau Adebowale, ya koka kan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari bai duba irin gudumawar da ya bai wa tsarikan tattalin arzikin kasar nan ba na tsawon shekaru 22.
Farfesa Adebowale a wata wasikar nuna takaicinsa da ya aikewa shugaban kasa, wacce Vanguard ta samu gani a Ibadan a ranar Lahadi, yace ya kwashe shekaru yana bada gudumawa ga gwamanti.
Peter Obi Ya Yi Magana Da CNN, Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Arewacin Najeriya Idan Ya Zama Shugaban Kasa
Ya fara hakan tun yana da shekaru hamsin kuma har yanzu da ya kai saba'in da biyu babu wata lambar yabo ko jinjina da aka taba bashi a kasar nan.
Adebowale ya jaddada cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Tsawon shekaru ashirin da biyu nake bai wa gwamnati gudumawa a fannin tsarikanta. Shawo kan tattalin arzikin kasar nan baya min wahala, ba zai yuwu wani ya maye gurbina ba kawai.
"Ina son shugaban kasa ya nada ni shugaban kwamitin farfado da tattalin arziki a maimakon mataimakin shugaban kasa. Na kwafi kungiyar kiristoci ta Najeriya. Mene ne CAN take yi yanzu?"
“Na fara lokacin da nake da shekaru hamsin, yanzu saba'in da biyu nake babu wata lambar yabo, babu wani abu da zan nuna don aikinsa.
"Ni na shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya daukar tsarin musamman na kananan 'yan sanda a 2018. Kuma gashi har wasu jihohi sun kaba. Har yanzu babu yabo ko godiya kan aikina."
- Yace.
Yadda Aka Titsiye Shugaban PSC, aka Tirsasa shi Yayi Murabus ana Tsaka da Taro
A wani labari na daban, tsohon sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Musiliu Smith, a jiya Laraba yayi murabus daga matsayinsa na shugaban hukumar kula da harkokin ‘yan sanda bayan rikicin da ya barke a hukumar.
Majiyoyi sun ce a taron shugabannin PSC da aka yi ranar Laraba, an bukaci Smith da yayi murabus kuma ya mika ragamar hukumar hannun mai shari’a Clara Ogunbiyi mai ritaya wacce ke wakiltar fannin shari’a a hukumar.
Asali: Legit.ng