Hatsarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar yarima Nuhu, matarsa, da 'ya'yansu hudu a hanyar Abuja

Hatsarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar yarima Nuhu, matarsa, da 'ya'yansu hudu a hanyar Abuja

- Allah ya yiwa ma'aikacin hukumar NCC, Yarima Nuhu Hammangabdo, da iyalinsa rasuwa a ranar Asabar

- Motar marigayin ta yi karo da wata mota kirar Siena a daura da garin Akwanga da ke jihar Nsarawa

- Marigayi Nuhu tare da iyalinsa - matarsa da 'ya'yansu hudu - suna kan hanyar komawa Abuja a lokacin da hatsarin ya afku

Ma'aikacin hukumar kula da kamfanonin sadarwa na kasa (NCC), Yarima Nuhu Hammangabdo, ya rasa ransa a wani hatsarin mota da ya ritsa da shi da iyalinsa.

Rahotan Dateline.ng bayyana cewa Yarima Nuhu ya na tare da matarsa, Hadiza Saidu Mairiga Nguroje, tare da 'ya'yansu hudu - Ummi, Ayman, Firdausi da Abdullah - a lokacin da hatsarin ya afku ranar Asabar.

A cewar wasu rahotanni, hatsarin ya faru ne sakamakon 'taho mu gamu' da wata mota kirar Siena da kuma motar da Yarima Nuhu ke ciki tare da iyalinsa, inda nan take suka kama da wuta.

KARANTA: Buhari da Osinbajo zasu karbi allurar rigakafin korona, za'a nuna a talabijin kowa ya gani

Hatsarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar yarima Nuhu, matarsa, da 'ya'yansu hudu a hanyar Abuja
Hatsarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar yarima Nuhu, matarsa, da 'ya'yansu hudu a hanyar Abuja @datelinenewsng
Asali: Twitter

Yarima Nuhu dan gidan sarkin masarautar Gashaka ne a jihar Taraba sannan matarsa kanwa ce wurin Babangida Nguroje, tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai.

KARANTA: Kwastam ta gano alburusai 5,200 da aka boye cikin wasu kaya, kudinsu ya haura N378m

Yarima Nuhu yana kan hanyarsa ta komawa wurin aikinsa a Abuja bayan ziyarar da ya kai mahaifarsa, karamar hukumar Gashaka, a lokacin da hatsarin ya faru a kusa da Akwanga, jihar Nasarawa.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa wasu 'yan bindiga sun yi harbe-harbe tare da tarwatsa jama'a a daidai katafaren shagon Ado Bayero Mall da ke kan titin zuwa gidan Zoo a birnin Kano.

Freedom Radio ta rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe goma na daren ranar Asabar.

A cewar rahoton da Freedom Radio ta wallafa, 'yan bindigar sun yi harbe-harbe a sararin samaniya, lamarin da ya saka jama'a gudun neman mafaka.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel