NIN: Yadda Kujerar Minista Ta Jawowa Isa Ali Pantami Barazanar Kisa a Najeriya

NIN: Yadda Kujerar Minista Ta Jawowa Isa Ali Pantami Barazanar Kisa a Najeriya

  • Isa Ali Ibrahim Pantami ya shigo da tsarin yin rajistar NIN a wayoyin salula domin a inganta tsaro
  • Wannan mataki da Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin kasar ya dauka, ya zo da irin farashinsa
  • Wasu sun fito suna barazana ga rayuwar Isa Ibrahim Pantami saboda yace dole ayi wa layin SIM rajista

Abuja - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami yayi bayanin kalubalen da ya fuskanta saboda ya kawo tsarin NIN.

A ranar Juma’a 16 ga watan Satumba 2022, Daily Trust ta rahoto Isa Ali Ibrahim Pantami yana cewa ya fuskanci barazanar kisa a kujerar Minista.

Pantami yace yunkurin yi wa kowane layin waya rajista da lambar NIN ta jawo masa wannan barazana.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Yi Magana Da CNN, Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Arewacin Najeriya Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Ministan ya bayyana haka ne a wajen wani taro na musamman da hukumar NIMC mai tattara bayanan ‘yan kasa ta shirya a birnin tarayya Abuja.

Barazana har a rediyo

A cewar Dr. Isa Pantami, ta kai an fito baro-baro a gidan rediyo ana yi masa barazana, ba don komai ba sai saboda ya shigo da tsarin yin rajistar NIN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Ministan ya fada, wannan baranza bai sa ya janye yunkurinsa ba domin ya san babu mai iko da rayuwar ‘Dan Adam sai Ubangiji.

Isa Ali Ibrahim Pantami
Isa Ali Ibrahim Pantami Hoto: ProfIsaPantami
Asali: Twitter

Jawabin Minista a taron NIMC

“Za mu cin ma nasara a bangaren tattalin arzikin zamani ne a lokacin da muka yi kokari wajen ganin mutane sun shiga cikin kundin bayanan kasa.
A lokacin da muka fara aikin nan, mutane da-dama sun juya mani baya. An yi wa rayuwata barazana a gidan rediyon BBC saboda shigo da tsarin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Buhari Ya Ɗauki Muhimmin Mataki Na Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

Na tsaya tsayin-daka domin nayi imani babu wanda ke da iko da rayuwata sai Allah madaukaki.

Kokarin da NIMC take yi a yau

Jaridar Leadership tace shugaban NIMC, Injiniya Aliyu Aziz ya gabatar da jawabi a wajen taron, ya yi bayanin yadda suke kokarin wayar da kan jama’a.

Aliyu Aziz yake cewa suna hada-kai da sarakunan gargajiya da masarautu domin mutane su san muhimmancin yin rajista katin NIN na ‘yan Najeriya.

Barazanar Boko Haram

A shekarun baya, an ji labarin yadda shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi barazanar kashe Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami da Bulama Bukarti.

Shekau ya bayyana haka ne a cikin wani sabon bidiyo daya fitar mai tsawon mintuna 15, ya caccaki Sheikh Isa Ali Pantami saboda tsarin da ya kawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng