Dan Jarida Mazaunin Kaduna Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ya Yanke Shawarar Ba Wa Ƴar Ekweremadu Kyautar Ƙodarsa

Dan Jarida Mazaunin Kaduna Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ya Yanke Shawarar Ba Wa Ƴar Ekweremadu Kyautar Ƙodarsa

  • John Femi Adi, wani dan jarida mazaunin jihar Kaduna ya sanar da cewa a shirye ya ke ya bawa yar Sanata Ekweremadu kyautar koda
  • Adi, wanda ya ce kuma shi manomi ne ya yanke shawarar bawa Sonia kodarsa kyauta ne saboda umurin Ubangiji na cewa 'mu so makwabtan mu kamar yadda muke son kan mu'
  • A baya-bayan nan, Sonia, ta fitar da sanarwa tana rokon al'umma su taimaka mata da koda domin rashin lafiya ya kama ta har ta dakatar da karatu

Kaduna - Wani dan jarida mazaunin Kaduna, John Femi Adi, ya yi alkawarin bada kodarsa daya ga Sonia, yar Sanata Ike Ekweremadu.

Ya sanar da hakan ne a wani rubutu da ya yi a Facebook mai taken "Niyyar ceton rai" a ranar Juma'a, 16 ga watan Satumba da safe.

Ekweremadu da Sonia da John
Dan Jarida Mazaunin Kaduna Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ya Yanke Shawarar Bawa Yar Ekweremadu Kyautar Kodarsa. Hoto: John Femi Adi/The Punch
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zan ba wa Sonia koda ta ne saboda umurnin Allah - Femi Adi

Adi ya yi bayanin cewa zai bada kyautar kodar ne saboda umurnin Allah na cewa mu rika kaunar makwabtan mu.

Ya rubuta:

"Ni, Kwamared John Femi Adi, dan jarida mai zaune a Kaduna kuma manomi ina sanar da niyya ta na bada koda na ga kyakyawar yar Sanata Ekweremadu.
"Ina yin hakan ne bisa umurnin Ubangiji a littafin Bible mai tsarki na cewa ku mu so makwabtan mu kamar yadda muka son kan mu.
"Don karin bayani, ana iya tuntuba ta a lambar waya ta kamar haka - 0803410833."

Wakilin Legit.ng Hausa ya samu tattaunawa da Mr John Femi Adi ta wayar tarho kuma ya masa wasu karin tambayoyi game da shawarar da ya yanke na bawa Sonia kodarsa daya idan har sun dace.

Da ya ke bada amsa kan tambayar da aka masa ko iyalan Ekweremadu sun tuntube shi kan batun, ya ce:

"Eh, gaskiya dai wasu mutane guda biyu sun kira ni da lamba (boyayya) daya da safe daya kuma da dare, suna son su tabbatar idan da gaske na ke yi domin wasu yan Najeriya suna fadan wasu abubuwa a intanet amma idan an nemi su sai a yi magana tsayayya sai su kashe bace.
"Na ce musu ni ba haka na ke ba, abin ya sosa min zuciya sosai cewa a cikin yan Najeriya fiye da miliyan 200 babu ko mutum daya ba da zai iya taimaka wa dan majalisa da ke mana aiki.
"Bana yi wa Ekweremadu kalon Ibo, ina masa kallon dan Najeriya ne kuma nima dan Najeriya ne, sannan ya dade yana yi wa kasar nan hidima da tabbatarwa cewa mun cigaba kuma mun samu hadin kai amma kowa noke wa."

Femi Adi ya cigaba da cewa wannan ba batun kudi bane, lamari ne na ceton rai kuma likitansa ya tabbatar masa mutum na iya rayuwa da koda daya.

Ya ce yana son ya zama misali ga sauran yan Najeriya cewa cikin mu akwai masu iya sadaukarwa don mu ceci wasu, 'ta fito fili ta yi roko, shi yasa nima na bayyana nawa a fili.'

Ba zan damu ko na mutu ba domin tarihi za ta tuna cewa na mutu don ceton wani kamar yadda Yesu almasihu ya mutu don ya cece mu, a cewarsa.

Iyaye na, yan uwa na da matata ta basu goyi baya ba - Femi Adi

Hakazalika, Mr Adi ya ce gaskiya yan uwansa ba su goyi baya ba a lokacin da ya fada musu don suna ganin tamkar zai jefa rayuwansa hatsari ne wurin ceton babban mutum zai iya siyan koda amma ya fahimtar da su fa'idar sadaukarwa da kuma daukaka sunan mahaifinsa ta hanyar aikata alheri.

Ya ce:

"Ka san mu yan Afirka ne, a kasashen yamma inda tunaninsu ya banbanta da namu za su iya fahimta idan na ce ina son ya bada koda.
"Wadanda suka fahimci inda na dosa sun karfafa min gwiwa, sun min addu'a kuma na yi alkawarin idan har kodar mu ta dace ku bar in bata domin da sunan mahaifina zan yi."

Daga karshe ya ce idan har likitoci sun tabbatar kodarsa zai dace da yar Ekweremadun, zai dawo ya bayyanawa duniya a shafinsa na Facebook cewa ya cika alkawari kuma an yi nasara.

Diyar Sanata Ekweremadu Ta Roki Al’ummar Annabi Su Taimaka Mata Da Koda

Tunda farko, kun ji cewa Sonia, diyar Sanata Ike Ekweremadu, ta roki jama’a da su taimaka mata da gudunmawar koda.

Diyar dan majalisar ta yi wannan rokon ne a daidai lokacin da iyayenta suka shiga tsaka mai wuya a kokarinsu na ceto rayuwarta.

An kama Ekweremadu da matarsa a watan Yuni lokacin da suke kokarin samawa Sonia gudunmawar koda daga wani matashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel