ObiDatti23: Lauyoyi 9 Sun yi Gayya, Sun Shigar da Karar Peter Obi da LP a Kotu
- Wasu mutane sun dauki hayar Lauya a kotu da nufin a dakatar da tattakin ‘#ObiDatti23 Forward Ever’
- Mabiya Peter Obi sun niyyar yin gangami na musamman domin nuna goyon bayansu ga ‘dan takaran LP
- Lauyan da ya shigar da kara yace yin wannan tattaki zai iya jawo a samu barkewar rashin zaman lafiya
Lagos - Wasu lauyoyi sun roki kotun tarayya mai zama a garin Legas da a hana tattakin da magoya bayan jam’iyyar LP suke shiryawa.
A rahoton da Premium Times ta fitar a yammacin Juma’a, an ji cewa wadannan lauyoyi suna neman kawo cikas ga shirin mabiya Peter Obi.
A ranar 1 ga watan Oktoba aka shirya tattakin ‘#ObiDatti23 Forward Ever’ a Legas domin nuna goyon baya ga Obi da Yusuf Datti Baba-Ahmed.
Lauyoyin sun nemi Alkali ya takawa Julius Abure da mutanensa burki daga yin wannan gangami sai lokacin da aka gama sauraron shari’a.
Lauyoyi 9 sun je kotu
Wadanda suka shigar da kara su ne: Adedotun Ajulo, Salamatu Suleiman Lewi, Hakeem Ijaduola, Ogunbona Akinpelu, da Owolabi Oluwasegun.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sauran lauyoyin sun hada da: Mogbojuri Kayode, Wuyep Mantim Nadom Esq., Dimimu Mabel, Kolawole Salami da kuma wani Wale Lawrence.
Dada Awosika SAN ne wanda ya tsayawa wadanda suke karar a gaban Alkali Daniel Osiagor.
Ana karar mutane 10
Rahoton yace wadanda za su kare kan su a shari’ar sun kunshi Peter Obi, Yusuf Datti Baba-Ahmed, Julius Abure, Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya.
Darekta Janar na DSS, kamfanin LCC, Kwamishinan ‘yan sandan Legas, Kwamishinan shari’a, da Gwamnan jihar suna cikin wadanda ake kara.
Awosika SAN ya fadawa kotu idan aka yi wannan tattaki, za a kawo rashin zaman lafiya a Legas kamar yadda aka gani da zanga-zangar #EndSARS.
Baya ga haka, jaridar This Day tace an roki Alkali ya haramtawa Peter Obi, Baba Ahmed, jam’iyyar LP da mabiyansu goyon bayan wannan yunkuri.
Daga cikin bukatun shi ne a hana ‘Yan LP amfani da wani wuri wajen yin zanga-zanga. An daga wannan shari’a zuwa 23 ga watan Satumban nan.
Boko Haram sun koma yakin gida
A kan batun tsaro, an ji labari baya ga luguden wuta da sojoji suke yi da jiragen Super Tucano a Arewa maso gabas, ‘Yan ta’adda sun shiga yaki da junansu.
Kowane bangare ya kwashi kashinsa a hannu a arangamar da aka yi tsakanin sojojin Abubakar Shekarau da ‘Yan ta'addan ISWAP a tsakiyar makon nan.
Asali: Legit.ng