Wahalar Man Fetur ta zo Karshe, An Tsaida Ranar da Za a Fara Tace Fetur a Gida
- Gwamnatin Tarayya ta tsaida lokacin da za a soma tace gangunan danyen man fetur a matatun Najeriya
- Ministan harkokin man fetur, Timipre Sylva yace ayyukan da ake yi a matatun kasar na tafiya da kyau
- Sylva ya bada tabbacin cewa kafin sabuwar shekara, matatar Fatakwal za ta rika tace ganguna 60, 000
Abuja - Akwai alamun cewa an kawo karshen wahalar man fetur da ake fama da ita a jihohin Najeriya, an yi nisa wajen aikin gyaran matatun kasar.
Rahoton da This Day ta fitar a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba 2022 yace gwamnatin tarayya ta tabbatar da za a gama gyara matatar Fatakwal.
Zuwa watan Disamban 2022 ake sa ran karasa aikin, matatar za ta fara tace danyen mai.
Karamin Ministan man fetur na kasa, Timipre Sylva ya yi wannan bayani a lokacin da ya zanta da manema labarai a fadar Aso Villa bayan taron FEC.
A sa’ilin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida, Sylva yace ana gyaran matatun man fetur da ke kasar nan, kuma za a kammala a lokacin da aka dauka.
An rahoto Ministan yana cewa da zarar an gama gyare-gyaren da ake yi, duk rana za a rika samun gangunan fetur 60, 000 daga matatar man Fatakwal.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daga Disamba za a fara tace mai
Tsohon gwamnan na jihar Bayelsa yace nan da karshen shekara, za a fara tace danyen mai a gida.
“Ana cigaba da aikin gyara matatun mai. Tsohuwar matatar da ke Fatakwal da zai iya aikin ganguna 60, 000 zai rika aiki daga Disamba.
Kuma za mu samu dama a lokacin aikin domin karasa gyaran sauran matatun Fatakwal.”
“Ayyukan gyaran matatun man garuruwan Kaduna da na Warri suna tafiya da kyau. Ba da dadewa ba za mu fara kai ziyarar gani da ido.
A jawabin da ya yi bayan taron majalisar FEC, Vanguard tace Ministan yace an amince da biyan N2.044b domin gina titi a kamfanin gas a Bayelsa.
Osinbajo zai wakilci Najeriya
Kun ji labari an aikawa manyan Duniya goron gayyatar janazar Elizabeth II, da alama Yemi Osinbajo ne zai wakilci Muhammadu Buhari a birnin Landan.
Babu tabbacin Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai samu zuwa jana’izar, kuma Birtaniya ba ta gayyaci kasashen Rasha, Myanmar, da Siriya ba.
Asali: Legit.ng