Jana’izar Elizabeth: An Gayyaci Shugabannin Duniya, Buhari Ba Zai Samu Zuwa ba

Jana’izar Elizabeth: An Gayyaci Shugabannin Duniya, Buhari Ba Zai Samu Zuwa ba

  • A ranar Litinin mai zuwa, 19 ga watan Satumba 2022, za a birne Marigayiya Sarauniya Elizabeth II a Birtaniya
  • Za a yi mata addu’o’i a babban cocin nan na Westminster Abbey da ke garin Landan, kasar Ingila, kafin a birne ta
  • Najeriya na cikin kasashen da aka gayyata, Farfesa Yemi Osinbajo zai halarci jana’izar a madadin shugaban kasa

Jaridar Telegraph ta kasar waje ta fitar da rahoto cewa shugabanni da manyan Duniya 500 aka gayyata zuwa jana’izar tsohuwar Sarauniyar.

Za ayi wa Elizabeth II addu’a a cocin Westminster Abbey wanda zai iya daukar mutane 2000 a lokaci guda, kuma a haska a gidajen talabijin.

Bisa dukkan alamu wannan ne mafi girman taro da Duniya za ta gani a tsawon shekaru masu yawa domin tun 1952 Elizabeth take kan karaga.

Daily Trust tace duk wani wanda yake da lambar girma na kasar Ingila zai samu damar halartar wannan taro, daga ciki har da masu farin hula.

Duka-duka, adadin wadanda aka aikawa goron gayyatar jana’izar sun kai mutum 1, 000. Kafin nan za su ci abinci tare da sabon Sarki Charles III.

Daga ranar Juma’a za a rufe kofar karbar goron gayyatar, a fara tsara yadda za a tsara wurin zama. Landan zai karbi manyan Duniya da iyalansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yemi Osinbajo
Yemi Osinbajo a Kenya Hoto: LaoluAkandeOfficial
Asali: Facebook

Wadanda za a gani a jana’izar

Sarki Charles III, gimbiya Anne, Yarima Andrew da Yarima Edward da iyalansu, Camilla, Sophie, Sir Tim Laurence, da Sarah Feguson za su je.

Za kuma a ga Jikokin Sarauniya - William, Harry, Peter Phillips, Zara Tindall, Beatrice, Eugenie, Louise Windsor, James, da Viscount Severn.

Shugabannin Birtaniya, Scotland, Amurka, Australiya, Faransa, da sauran kasashen Turai da shugabannin Jafan, Koriya da irinsu Qatar duk za su je.

Birtaniya ba ta gayyaci Vladimir Putin na Rasha da shugabannin kasashen Venezuwala, Siriya, Belarus da Myanmar zuwa taron jana’izar ba.

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan yace zai je idan ya samu sukuni.

An gayyaci Najeriya

Wata majiya daga fadar shugaban Najeriya tace Farfesa Yemi Osinbajo ne wanda zai wakilci Mai girma Muhammadu Buhari Westminster Abbey.

Mafi yawan shugabannin kasashen da za su je kasar Ingila za su bi jirgin kasuwa ne, kuma za a rika daukar su ne a cikin mota a Birnin Landan.

Za a kashe Biliyoyi

Ku na da labari bikin birne Sarauniyar Ingila da bikin nadin sabon Sarki Charles III zai jawo Gwamnatin Birtaniya ta kashe kusan Dala Biliyan 7.

Ana kukan za ayi facaka da kudin da ya isa a ciyar da ‘yan makaranta fiye da miliyan 3 wajen jana'izar Sarauniya Elizabeth II da ta cika a makon jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel