Zan So In Ga Mace Ta Zama Shugaban Kasa A Najeriya, In Ji Gwamnan PDP

Zan So In Ga Mace Ta Zama Shugaban Kasa A Najeriya, In Ji Gwamnan PDP

  • Gwamna Udom Gabriel Emmanuel na Jihar Akwa Ibom ya ce yana fatan wata rana mace za ta zama shugaban kasa a Najeriya
  • Jigon na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya furta hakan ne a ranar Alhamis a yayin da matan gwamnoni suka kai masa ziyara a gidan gwamnati a Uyo
  • Amma, Gwamna Emmanuel ya koka kan yadda matan suke jan kafa wurin fitowa neman takarar shugabancin kasa inda ya bada misali ta zaben fidda gwani na (PDP) da aka yi a baya-bayan nan

Akwa Ibom - Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Gabriel Emmanuel, ya ce zai da ce a ga mace tana jagorantar Najeriya a matsayin shugaban kasa a nan gaba, rahoton Premium Times.

Mr Emmanuel ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Uyo lokacin da matan gwamnonin jihohin Najeriya suka ziyarce shi a gidan gwamnati, Uyo, Jihar Akwa Ibom.

Gwamna Emmanuel
Ina Son Ganin Mace Ta Zama Shugaban Kasa A Najeriya, In Ji Gwamnan PDP. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Tsakani da Allah, zan so in ga shugaban kasa mace a Najeriya, mu ga yadda hakan za ta kasance."

Mr Emmanuel, amma ya ce ya hangi wani abu da zai kawo tangarda game da yiwuwar hakan.

Ya ce:

"Amma matsalar shine idan mu tafi yin zabukan fidda gwani, ba mu cika ganin mata suna fitowa ba.
"Gwamnoni da dama sun fito domin takarar shugaban kasa (a zaben fidda gwani na karshe), ban ga matan gwamnoni sun fito ba. Ta yiwu lokacin da muke lissafi, ko lokacin da muke neman yin sulhu, watakila za mu zabi daya cikin matan gwamnonin a matsayin shugaban kasa na gaba."

Gwamna Emmanuel ya yi murmushi a lokacin da mahalarta taron suka tafa masa.

Abin Da Muka Tattauna Da Obasanjo, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Accord Party, AP, Farfesa Christopher Imumolen ya bayyana abin da suka tattauna da tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Aremu Mathew Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ba wannan bane karo na farko da mai fatan zama shugaban kasar ya ziyarci tsohon shugaban kasar.

Yayin ziyarar, hotuna sun nuna farfesan ya rusuna kan gwiwansa yayin da Obasanjo ke masa addu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel