Gwamna Zulum Na Borno Ya Yi Muhimmin Nadi A Gwamnatinsa
- Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da nadin Baba Bura Usman a matsayin sabon akanta janar na Jihar Borno
- Malam Isa Gusau, mai magana da yawun gwamnan na Jihar Borno ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba
- Baba Bura Usman, wanda kwararre ne a bangaren kudi zai maye gurbin Mai Adamu Ya'u wanda ya yi murabus a baya-bayan nan
Borno - Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya amince da nadin Baba Bura Usman a matsayin sabon akanta janar na Jihar Borno.
Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Laraba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kafin nadinsa, Bura shine direktan fanin ajiyar kudi a Ma'aikatar Kudi da Tsare-Tsare na Jihar Borno tun shekarar 2020 in ji Gusau.
Usman, dan shekara 57, dan asalin karamar hukumar Kaga ne a arewacin Borno, ya shafe kimanin shekara 20 yana aiki a bangaren kudi a cewar sanarwar.
Wasu daga cikin wuraren da Usman ya yi aiki a baya
Ta kara da cewa akanta janar din, tun 1990, ya yi aiki a matsayin mataimakin akanta a wani kamfani mai zaman kansa, Premier Property Dev. Co. Ltd, kafin ya fara aiki da gwamnatin jihar Borno a matsayin babban akanta a Cibiyar Al'adu da ke Maiduguri a 1998.
Usman ne babban akanta a gidan gwamnati a Maiduguri a 2021 kuma shine babban akanta a sashin kasafi da tsare-tsare a 2003, a Hukumar Ilimi Bai Daya Na Borno a 2010 da kuma Hukumar Fansho ta Borno a 2017 kafin ya zama direkta a hukumar fansho a 2017, a cewar sanarwar.
Usman ya kuma yi wasu ayyukan da dama a ma'aikatu da hukumomin gwamnatin a Borno.
Takaitaccen tarihin karatun Usman
Usman yana da babban diploma ta kasa (Hnd) a bangaren kula da kasuwanci daga Kwalejin Ilimi Ta Ramat, Maiduguri.
Usman ya yi kwasa-kwasai a bangaren kula da kudade a Najeriya da Hadadiyar Daular Larabawa, UAE, kuma yana da satifiket a bangaren kula da kudade, fasahar sadarwa da akanta ,IPSAS, da ilimin kwamfuta.
Sabon akanta janar din kuma mamba ne a kungiyar akantoci ta Najeriya (ANAN) da wasu kungiyoyin.
Usman zai karbi aiki ne daga hanun Mai Adamu Ya'u wanda ya yi murabus a baya-bayan nan.
Borno: Zulum Ya Biya Naira Miliyan 5 Don Daukan Nauyin Karatun Wani Hazikin Yaro Mai Shekara 13 a Maiduguri
A wani rahoton, Gwamna Zulum na Jihar Borno ya bada N5m ga wata makaranta mai zaman kanta domin daukan nauyin karatun Musa Sani, yaro dan shekara 13 mai hazaka a Borno wanda ya yi amfani da laka ya kwaikwayi ginin gadan sama ta farko a jihar da ke custom round about a Maiduguri.
An biya kudin ne ga hukumar makarantar Golden Olive Academy, Maiduguri, domin daukan nauyin karatun Musa daga ajin frimare na hudu har kammala babban sakandare, Nigerian Tribune ta rahoto.
Asali: Legit.ng