Hukumar JAMB na neman a bata cikakken ikon cin gashin kai, a cire ta daga kasafin kudin kasa

Hukumar JAMB na neman a bata cikakken ikon cin gashin kai, a cire ta daga kasafin kudin kasa

  • Gwamnattin Najeriya ta rage kudin jarrabawar JAMB a shekarar 2017, amma hukumar ta nemi a kara kudin jarrabawar
  • Hakazalika, shugaban JAMB ya ce ya kamata a bar hukumar take cin gashin kanta, kana a cire ta daga kasafin kudi
  • Sai dai, jami'o'in da JAMB din ke tura dalibai sun shafe akalla watanni shida a garkame saboda yajin aikin ASUU

FCT, Abuja - Shugaban hukumar jarrabawar shiga jami'a ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bukaci majalisar wakilai da ta baiwa hukumar ikon cin gashin kanta ta fannin kudi tare da cire ta daga kasafin kudin gwamnati.

Oloyede ya yi wannan roko ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan kudirin kasafin kudi na MTEF a yau Laraba 14 ga watan Satumba.

JAMB na neman cin gashin kanta, ta bar karkashin gwamnati
Hukumar JAMB na neman a bata cikakken ikon cin gashin kai, a cire ta daga kasafin kudin kasa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sai dai, ya ce daya daga cikin sharuddan da aka daurawa hukumar shi ne ta sake duba kudaden jarrabawa tare da kara su, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano Ta Gana Da ASUU, Ta Bukaci Su Janye Yajin Aiki A Jami'o'in Jihar

Ya ce hukumar ta JAMB ta rage kudin rajistar yin jarrabawar shiga jami'a daga N5,000 zuwa N3,500 a 2017 bayan da ta tura Naira biliyan 7.5 a asusun gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai bukatar a kara kudin jarrabawar JAMB, inji hukumar

Shugaban ya ce, duba da matsin tattalin arziki da gwamnatin Najeriya ke fuskanta, ya kamata JAMB ta koma karbar N5,000 na rajista kamar yadda yaake a baya kuma ta zama mai cin gashin kanta.

A cewarsa, kasar Finland ce kadai kasar da ke karbar kudin jarrabawar shiga jami'a kamar Najeriya, Premium Times ta ruwaito.

Ya kara da cewa, babu wata kasa a duniya banda kasashen biyu dake biyawa 'yan kasarta kudin jarrabawar shiga jami'a.

Yadda Yajin Aikin ASUU Ya Maida Dalibin Likitanci Mai Siyar da Abinci a Jihar Sokoto

A wani labarin, Usman Abubakar-Rimi, wani dalibin ajin karshe a fannin likitanci a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (UDUS) ya bayyana yadda ya fara sana'ar abinci a kan saboda tsawaitar yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa ga Gwamnoni: Motocin da Harsasai Basu Hudawa ba Zasu Kare ku daga Fushin Yaran Talakawa ba

Idan baku manta ba, ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun bana, inda ta kora dalibai gidan iyayensu tare da maida su 'yan zaman kashe wando, Daily Trust ta ruwaito.

Abubakar-Rimi ya ce zama bai kama shi ba, domin dole ya nemi abin yi domin kashe lokaci da kuma iya daukar nauyin rayuwa da dai sauran abubuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.