2023: Babu Gudu Babu Ja Da Baya Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi, Shugabannin CAN Na Arewa

2023: Babu Gudu Babu Ja Da Baya Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi, Shugabannin CAN Na Arewa

  • Shugabannin kungiyar kirista ta Najeriya CAN na jihohin arewa sun jadada matsayarsu na kin goyon bayan tikitin musulmi da musulmi na APC
  • Shugabannin kiristcin sun sanar da hakan ne bayan wani taron sirri da suka yi a Abuja a ranar Talata da ya samu hallarcin ciyamomin CAN na jihohin arewa
  • Rabaran Hayat, shugaban CAN na Kaduna ya ce za su yi taro da yan siyasa kiristoci su tsayar da wadanda za su goyi baya amma banda jam'iyya mai tikitin musulmi da musulmi

Abuja - Ciyamomin kungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN, suna cigaba da nuna rashin amincewarsu da tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyar APC ta yi, tana cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba a yunkurinta na neman adalci.

Sun jadada wannan matakin nasu ne a ranar Talata a taron sirri da jiga-jigan APC biyu, Hon Yakubu Dogara da Babachir Lawal suka kira a Abuja.

Kara karanta wannan

Buhari ya magantu, ya ce akwai wadanda ya kamata suke tallata gwamnatinsa amma ba sa yi

Taron CAN a Abuja
2023: Babu Gudu Babu Ja Da Baya Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi, Shugabannin CAN Na Arewa. Hoto: @YakubDogara.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dogara, wanda tsohon kakakin majalisar wakilai na tarayya ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter.

Idan za a iya tunawa, Asiwaju Bola Tinubu, musulmi ya zama dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023 kuma ya zabi Kashim Shettima, shima musulimi kuma tsohon gwamnan Borno a matsayin abokin takararsa.

Amma Dogara ya ce an yi taron ne da shugabannin kiristocin daga arewa da Abuja don yanke shawara kan tawagar masu kishin Najeriya gabanin zaben 2023.

Ya rubuta:

"#NigeriaDecides2023- Ana cigaba da yakin tabbatar da adalci. Yau mun yi taron tuntuba da shugabannin kiristoci daga jihohin arewa 19 da FCT kan tsarin kishin Najeriya a 2023."

Shugaban CAN na Kaduna ya tabbatar da taron

Yayin da ya ke tabbatarwa Vanguard ta taron, shuugaban CAN na Kaduna, Rabaran John Hayan ya ce:

Kara karanta wannan

Tashin hankali ga 'yan Najeriya yayin da Buhari yace zai haramta amfani da kananzir

"Dukkan shugabannnin CAN na arewa, illa na Katsina sun hallarci taron.
"Muna cewa babu ja da baya kan matakin mu na kin amincewa da tikitin musulmi da musulmi na APC."

Da aka masa tambaya kan jam'iyyar da shugabannin kiristocin na arewa za su mara wa baya, Hayab ya ce:

"Za mu yi taro da manyan yan siyasa kiristoci a jam'iyyu kafin mu yanke shawarar matakin da za mu dauka a gaba.
"Za mu jira sako daga shugaban CAN na kasa. Su ma za su nuna mana inda ya dace mu bi amma maganar tikitin musulmi da musulmi ba mu tare da shi.
"Abin da muka yi tsammani shine APC za ta kira shugabannin kiristoci ta musu bayani a maimakon dauko hayan wasu su yi shiga irin ta shugabannin kirista."

2023: Ƙungiyar Mayu Da Matsafa Ta Najeriya Ta Yi Magana Mai Ƙarfi Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC

A wani rahoton, Cif Okhue, kakakin kungiyar Fararen Mayu da Matsafa ta Najeriya (WITZAM), ya ce babu wani matsala don jam'iyyar APC ta tsayar da musulmi biyu a takarar shugaban kasa da mataimaki.

Kara karanta wannan

Rikici ya kunno: An Zargi Shugaban Matasa da Fifita Yarbawa a Taron Jam’iyyar APC

Ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke bayyana cewa nan bada dadewa ba kungiyar za ta hango wanda zai zama shugaban kasa a 2023, Independent ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel