'Ka Dai Ji Kunya' Gwamna Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Ministan Buhari Mai Murabus

'Ka Dai Ji Kunya' Gwamna Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Ministan Buhari Mai Murabus

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya caccaki tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yace ya kai maƙurar gazawa
  • Da yake martani kan wasu kalaman Amaechi, Wike yace ya fito ya faɗi ayyukan da ya yi wa Ribas tsawon shekara 7 yana madafun iko
  • Amaechi ya zargi gwamnatin Wike bisa gazawa wajen gudanar da jana'izar girma ga wani dattijon jiha da ya rasu

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da wanda ya kai maƙurar gazawa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da yake jawabi a wurin kaddamar da ginin tsohon Riv Bank Insurance da gwamnatinsa ta Sabunta a Patakwal ranar Litinin, Wike ya zargi tsohon ministan da gaza taɓuka wa al'ummar ribas komai tsawon shekaru 7.

Kara karanta wannan

Taraba: Dubban jama'a sun yi wa Nyame maraba bayan Buhari yayi masa rangwame

Gwamna Wike da Amaechi.
'Ka Dai Ji Kunya' Gwamna Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Ministan Buhari Mai Murabus Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Yace mutumin da ya gaza kawo ayyuka jiharsa abinda ya kamace shi ya rufe fuskarsa saboda tsabagen kunya kana ya daina tsoma baki kan harkokin siyasar Ribas.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin raddi kan kalaman tsohon ministan cewa gwamnatin Ribas bata kyauta ba bisa rashin gudanar da Jana'izar marigayi Chief Alabo Tonye Graham-Douglas, wanda aka binne karshen mako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun kwashe dukkan mutanen ku, babu kowa a jam'iyyar ku a yanzu, meyasa ba zaka jure ka yi gum da bakinka ba saboda gazawar gwamnatinku."
"Ka faɗa wa al'ummar jihar Ribas, a matsayin daka dafe na ministan Sufuri, me ka yi musu? Bamu ga ko kwara ɗaya ba daga Patakwal zuwa Maiduguri."

- Gwamna Wike

Wike ya bugi ƙirjin cewa lokacin yana ƙaramin Ministan, ya jawo an gina tsangayar koyar da ilimin shari'a a Jami'ar Patakwal, sannan aka gina Oil And Gas Poly Aa Bonny.

Kara karanta wannan

Akwai Aiki A gaba: Sanatan PDP Ya Bayyana Abun Da Zai Faru Idan Ayu Ya Yi Murabus

"Ka faɗa mana a matsayin minista na matakin farko me ka tsinana mana? Kana tsammanin zaka sake yaudarar mutanen Ribas ne a yanzu?"

Meyasa Gwamnatin Wike babta girmama mutumin ba?

Gwamnan ya yi bayanin cewa gwamnatinsa ta tsame kanta daga bikin binne gawar ne ganin an maida lamarin tamkar siyasa kuma ba ya son shiga irin waɗannan harkokin.

A rahoton Punch, gwamna Wike ya cigaba da cewa:

"Na gano kun snaya siyasa da bikin Jana'izar mutumin. Ni kuma na yanke janye jikina, bana son jefa kaina cikin wannan siyasa."
"Na yi mamakin cewa tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yana da bakin zuwa ya yi magana kan gwamnatin Ribas ta gaza gudanar da Jana'izar girma ga Alabo Tonye Graham-Douglas."
"Lokacin da yake jinya kana ina? Gwamnatin mu ta yi duk me yuwuwa da kuɗinta don ganin ya rayu. Ina kalubalantar kowa, mun kashe abinda bai gaza miliyan N50m ba domin ceto rayuwarsa."

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Kotu Bayan Sun Gaza Cimma Matsaya A Tattaunawarsu

A wani labarin kuma Gaskiya Ta Fito Game da Ƙishin-Kishin Din Kwankwaso Zai Janye Wa Atiku ko Tinubu a 2023

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta rahoton dake cewa yana duba yuwuwar janye wa Atiku ko Tinubu.

Mai magana da yawun tawagar kanfen din Kwankwaso, Ladipo Johnson, yace ya kamata yan Najeriya su daina ɗaukar kowake zance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel