Ruwan wutar sojin sama a maboyar mayakan kungiyar Boko Haram ya hallaka Matar Shekau Firdausi

Ruwan wutar sojin sama a maboyar mayakan kungiyar Boko Haram ya hallaka Matar Shekau Firdausi

- Sojojin sama sunyi luguden wuta a maboyar mayakan kungiyar Boko Haram

- Rundunar sojin saman ta bayyana cewar ruwan wutar data yi ya rutsa da uwargidan Shekau

- Hukumar sojin ta bayyana cewar har yanzu tana kokarin tantance gawar Firdausi

Kamar yadda muka kawo muku rahoton kaddamar da ruwan wuta da hukumar sojin sama ta yi a wasu daga cikin maboyar mayakan kungiyar Boko Haram, rahotanni na nuni da cewar cikin wadanda suka rasa ransu har da uwargidan shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau.

Ruwan wutar sojin sama a maboyar mayakan kungiyar Boko Haram ya hallaka Matar Shekau Firdausi
Ruwan wutar sojin sama a maboyar mayakan kungiyar Boko Haram ya hallaka Matar Shekau Firdausi

Sanarwar da rundunar sojin saman ta saki, ta bayyana cewar ruwan wutar data yi ya rutsa da uwargidan Shekau din ne yayin da take wakiltarsa a wani taron manyan kwamandojin kungiyar a daya daga cikin maboyar tasu.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Boko Haram ta kai hari a Yobe

Sojojin sama sunyi luguden wuta a maboyar mayakan kungiyar Boko Haram dake Durwawa daura da Urga dake Konduga a ranar 19 ga wannan watan. Harin na hukumar sojin sama dai ya hallaka mayakan kungiyar Boko Haram da da dama.

Hukumar sojin ta bayyana cewar har yanzu tana kokarin tantance gawar Firdausi daga cikin ragowar gawarwakin mayakan kungiyar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng