Jerin Kasashe 10 a Afirka da Suka Fi Ko’ina Tsadar Man Fetur a 2022

Jerin Kasashe 10 a Afirka da Suka Fi Ko’ina Tsadar Man Fetur a 2022

  • Najeriya, kasa mai arzikin man fetur bata daya daga cikin kasashen Afrika dake da tsadar farashin man fetur
  • Wasu kasashen da ba sa samar da man fetur sun fito a jerin kasashen dake da farashi mai tudu na man fetur
  • Najeriya ta sanar da cewa, a watan Yunin 2023 za ta cire tallafin man fetur, lamarin da ya jawo cece-kuce a kasar

Farashin man fetur sai tashi yake a nahiyar Afrika, musamman tun bayan fara yakin Rasha da Ukraine a watan Fabrairu.

A watan Maris, Najeriya ta fuskanci wani mummunan yanayi na karancin man fetur tun bayan da kasar ta shigo da wani nau'in mai gurbatattce.

Yadda ake fama da tsadar mai a wasu kasashen Afrika
Jerin Kasashe 10 a Afirka da suka fi ko'ina tsadar man fetur a 2022 | Hoto: itnewsafrica.com
Asali: UGC

Kamfanin man fetur na NNPC ya ce an shiga karancin man fetur ne a Maris sakamakon tacewa da tsaftace man da kamfanin ke yi.

Kara karanta wannan

Amurka Na Neman Wani Dan Najeriya Ruwa A Jallo, Ta Bayyana Dalili

Duk da karanci da tsadar da Najeriya ta fuskanta a shekarar nan, bata cikin jerin kasashen da ke fama da tsadar mai saboda tallafin da gwamnati ke sanyawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Silar tashin farashin man fetur

A cewar wani rahoton Reuters, Najeriya za ta kashe N6.7tr a shekara mai zuwa da sunan tallafin man fetur.

Rahoton ya ce, akwai tunani da hasashen yiwuwar kara haihawar farashin man fetur a nahiyar Afrika kuma hakan zai yi matukar tasiri ga kasashen.

Kasancewar Rasha cikin kasashen dake da tasiri wajen fitar da man fetur, an ce akwai takunkumin da aka sakawa kasar zai shafi samuwar fetur a duniya, rahoton Business Insider.

Kasashe masu tsadar mai a Afrika

  1. Zimbabwe - $2.153
  2. Seychelles - $1.541
  3. Malawi - $1.426
  4. Uganda - $1.389
  5. Mauritius - $1.381
  6. Burundi - $1.340
  7. Senegal - $1.299
  8. Lesotho: - $1.231
  9. Rwanda - $1.230
  10. South Africa - $1.413

Kara karanta wannan

Hotunan Atamfofin da 'Yan Najeriya Suka Fitar Matsayin Ankon Bikin Mutuwar Sarauniyar Ingila

Akalla ₦462 Za'a Fara Siyar Da Litan Mai Idan Aka Cire Tallafi Bayan Zaben 2023, NNPC

A wani labarin, idan aka cire tallafin mai a watan Yuni 2023 kamar yadda ake shirin yi, za'a koma sayar da Litan Mai ₦462, Kamfanin man feturin Najeriya (NNPC) ya bayyana hakan ranar Lahadi.

Kamfanin ya bayyana cewa farashin kudin ton 1 na mai a kasuwar duniya yanzu $1,283 ne.

Idan akayi lissafin kudaden, farashin kudin litan mai ya zama N462, yayinda ake biyan tallafin N297 kan kowani lita, za'a kashe N6.5 trillion a shekara kan tallafin man litan milyan 60 da ake sha kullum a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.