Akalla ₦462 Za'a Fara Siyar Da Litan Mai Idan Aka Cire Tallafi Bayan Zaben 2023, NNPC

Akalla ₦462 Za'a Fara Siyar Da Litan Mai Idan Aka Cire Tallafi Bayan Zaben 2023, NNPC

  • Kamfanin man fetur na NNPCL ya mayar da martani ga Hameed Ali, Shugaban hukumar Kwastam
  • NNPC ya jaddada cewa lallai litan mai milya sittin da takwas ake sha kulli yaumin a Najeriya
  • Shugabannin NNPC bayyanawa Kanar Hameed Ali shirye su a gudanar binciken kwakwaf kan lamarin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Idan aka cire tallafin mai a watan Yuni 2023 kamar yadda ake shirin yi, za'a koma sayar da Litan Mai ₦462, Kamfanin man feturin Najeriya (NNPC) ya bayyana hakan ranar Lahadi.

Kamfanin ya bayyana cewa farashin kudin ton 1 na mai a kasuwar duniya yanzu $1,283 ne.

Idan akayi lissafin kudaden, farashin kudin litan mai ya zama N462, yayinda ake biyan tallafin N297 kan kowani lita, za'a kashe N6.5 trillion a shekara kan tallafin man litan milyan 60 da ake sha kullum a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ni Fa Ban Yarda Da Kudin Tallafi N6tr Da NNPC Tace Tana Biya Ba, Shugaban Kwastam Hameed Ali

NNPC yace shirye yake a gudanar da bincike kan tabbatar da gaskiyar adadin man da ake sha a Najeriya.

Shugaban sashen yada labarai na NNPC, Mallam Garba Deen Muhammad, ya bayyana a jawabin da ya fitar.

Yana martani ne kan kalaman kwantrola janar na hukumar Kwastam, Hameed Ali, kan rashin amincewarsa na adadin litan man da ake sha a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mele Kyari
Kudi ₦462 Za'a Fara Siyar Da Litan Mai Idan Aka Cire Tallafi Bayan Zaben 2023, NNPC Hoto: NNPC
Asali: Facebook

Ni Fa Ban Yarda Da Kudin Tallafi N6tr Da NNPC Tace Tana Biya Ba, Shugaban Kwastam Hameed Ali

Kwantrola Janar na hukumar hana fasa kwabri watau Kwastam, Hameed Ali, a ranar Alhamis ya nuna rashin yardarsa da N6tr da gwamnati ke ikirarin ta kashe kan tallafin mai a 2022.

Hameed Ali ya bayyana hakan yayinda ya bayyana gaban kwamitin kudi na majalisar wakilan tarayya, rahoton Tribune.

Ya ce maganar cewa ana shan litan man fetur 98 a rana karya ne, lita milyan 38 fitar da shi ake kasashen waje.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya Nada Yayan Aisha Buhari Matsayin MD na NSPMC

Zamu Karbi Sabon Bashin N11tr Kuma Zamu Sayar Da Wasu Dukiyoyin Gwamnati A Shekarar 2023, Minista Zainab

Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata karbi sabon bashin sama da N11 trillion tare da sayar da dukiyoyin gwamnati don kasafin kudin 2023.

Ta bayyana cewa gwamnati zata bukaci kudi N12.42 Trillion idan har zata cigaba da biyar tallafin mai a 2023.

Hajiya Zainab ta bayyana hakan ne ranar Litnin yayinda ta bayyana gaban yan majalsar wakilai

Asali: Legit.ng

Online view pixel