Mutanen Gari Sun Ga Tashin Hankali, An Yi Garkuwa da Wani Basarake a Najeriya

Mutanen Gari Sun Ga Tashin Hankali, An Yi Garkuwa da Wani Basarake a Najeriya

Labari mara dadi ya zo cewa masu garkuwa da mutane sun dauke Mai martaba, Cif Eze Jewel Ndenkwo

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Eze Jewel Ndenkwo Sarki ne a karamar hukumar Nkwerre a jihar Imo, a gaban ofishinsa aka dauke shi

Tun da abin ya faru, kusan sa’a 24 kenan amma ba a ji ‘yan bindigan sun tuntubi ‘yanuwan Basaraken ba

Imo - Wasu da ake zargin miyagun ‘yan bindiga ne sun dauke Mai martaba Eze Jewel Ndenkwo wanda Basarake ne a jihar Imo.

Punch tace Basaraken shi ne shugaban manyan kamfanoni irinsu Udekings Nigeria Limited da ake aiki a yankin kudancin Najeriya.

An dauke Eze Ndenkwo ne a gaban wani kamfaninsa da ke babban birnin Owerri, jihar Imo.

Basaraken shi ne yake rike da kasar Isiala Umudi a karamar hukumar Nkwerre, abin ya faru ne da kimanin karfe 7:00 na Juma’a.

Kara karanta wannan

Ku Daina Yaudarar Mutane: Jigon APC Yana Neman Cirewa Tinubu Zani a Kasuwa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda aka yi Inji wani mazauni

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa abin ya faru ne a gaban wani ofishin Mai martaban a unguwar Tetlow a yammacin jiya.

Tun da abin ya faru, har yanzu ‘yan binigan ba su tuntubi iyalin Basaraken ba, kamar yadda aka san al’adar masu garkuwa da mutane.

'Yan Sanda
'Yan Sandan Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An yi haka - Gwamnatin Imo

Rahoton Daily Trust yace an tuntubi Kakakin ‘yan sanda na jihar Imo, CSP Micheal Abattam domin jin ta bakinsa, amma shiru.

Yayin da ake sauraron Micheal Abattam, gwamnatin jihar Imo ta tabbatar da abin da ake tsoro.

Kwamishinan yada labarai da dabaru na Imo yace abin ya faru, kuma gwamnati tana kokarin kawo karshen ta’adin da ke faruwa a jihar.

Karin bayanin da muka samu shi ne ana haka kuma sai aka dauke wasu Bayin Allah da suka halarci wani bikin aure a garin Isiala Mbano.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan PDP Ya Fito Baro-baro, Gwamnoni 8 Sun Ki Zuwa Taron Jam’iyya

Wadanda aka yi garkuwa da su sune; Collins Alaefula, Mmadu Promise da Victor Chibuike, an ji cewa sun fito bayan sun biya kudi.

DSS a gidan Tukur Mamu

Bayan an cafke Tukur Mamu, sai ga labari cewa dakarun DSS sun yi motoci zuwa gidan ‘dan jaridar a garin Kaduna, suka bincike ko ina.

Ana kwance sai iyali suka ji ma’aikatan tsaro masu fararen kaya sun dura gida da ofishin mawallafin Desert Herald, Malam Tukur Mamu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng