Tsohon Tarihi: Yadda Elizabeth II Ta Takawa Buhari Burki Shekaru 38 da Suka Wuce

Tsohon Tarihi: Yadda Elizabeth II Ta Takawa Buhari Burki Shekaru 38 da Suka Wuce

  • Marigayi Shehu Shagari ya taba kai wa Sarauniya Elizabeth II ziyara tare da wasu na kusa da shi a mulki
  • A cikin tawagar Shugaba Shagari akwai Umaru Dikko da Chuba Okadigbo, Isyaku Ibrahim ya bada labarin
  • A lokacin da aka yi yunkurin dauke Dikko daga Ingila, Sarauniyar ta taimaka wajen hana a kai ga nasara

Abuja - A ranar Juma’ar nan da ta wuce, Dattijon nan kuma tsohon ‘dan siyasa, Alhaji Isyaku Ibrahim ya yi magana a kan rasuwar Sarauniya Elizabeth II.

Isyaku Ibrahim ya zanta da Daily Trust, ya yi masu bayanin wasu daga halin Marigayiyar domin ya taba samun damar alaka da Elizabeth da tana raye.

Tsohon ‘dan siyasar yace mutuwar Basarikiyar ta girgiza shi domin ba a dade ba da Elizabeth II ta zauna da sabuwar Firayim Ministar Birtaniya, Liz Truss.

Ibrahim yace ya san abubuwa da-dama a game da marigayiyar domin a lokacin da Alhaji Shehu Shagari ya kai mata ziyara a fadarta, yana cikin tawagarsa.

Shagari a Fadar Birtaniya

“Jami’ai hudu kurum aka ba su zauna da Shagari a fadar Buckingham. Akwai Dr Umaru Dikko, Dr Chuba Okadigbo, sai kuma Hon. Idrisu Ibrahim Kuta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“An tarbi Shagari da kyau, amma wasunmu ba su zauna a fadar ba. Ni ina da gida a Landan, Shettima Ali Monguno yana auren ‘Yar kasar Birtaniya.
Elizabeth II
Shehu Shagari da Elizabeth II Hoto : autojosh.com
Asali: UGC

Shettima Ali Monguno da Shagari abokai ne sosai, dukkaninsu malaman makaranta ne, kuma sun yi aiki tare da Gowon a lokacin yana shugaban kasa.

A cewar Isyaku Ibrahim, Sarauniyar Ingilar ta san Shagari ya zo da tawaga da yawa, sai ta sa aka shirya masu abinci, ta kuma karbe su ana wasa da raha.

A wurin Shagari ya ambaci sunayen ‘yan tawagarsa, sai yace Monguno surukinta ne domin yana auren Ba’Ingila, Ibrahim yace shi yana auren Baleberiya.

Baya ga haka, Ibrahim ya san Sarauniya a Mijinta domin ya samu aiki a ofishin jakadanci a matsayin malamin bayanai bayan ya gama karatu a Jamus.

Rikicin Gwamnatin Buhari da Dikko

Datiijon yace Marigayiyar ta taka rawar gani a lokacin da gwamnatin soja tayi yunkurin dauko Umaru Dikko daga Ingila domin a maida shi Najeriya.

Kamar yadda aka rahoto, da ya samu labarin an dauke Umaru Dikko, sai ya kira wani abokinsa, har maganar ta kai zuwa fadar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II.

Nan take Marigayiya Elizabeth II tayi ihu, tace Dikko ya taba zaba bako a fadarta, ta tuntubi Margaret Thatcher, wannan ya hana a dauke Dikko daga Ingila.

Charles ya zama Sarki

Kun samu labari cewa babban ‘dan Sarauniya Elizabeth II da Prince Philip ya dare kan karagar gidan sarautar Birtaniya bayan Sarauniyar ta bar Duniya.

Sarki Charles III ya gaji mahafiyarsa wanda ta rasu bayan tayi shekaru 70 tana kan mulki a kasar Ingila. Elizabeth II ta rasu tana mai shekara 96 da haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel