Yan Sanda Sun Kama Isiyaku Babangida, Kasurgumin Dan Bindigar Zamfara Da Ake Nema Ruwa A Jallo

Yan Sanda Sun Kama Isiyaku Babangida, Kasurgumin Dan Bindigar Zamfara Da Ake Nema Ruwa A Jallo

  • Jami'an rundunar yan sanda a jihar Zamfara sun kai samame mabuyar wasu yan ta'adda da suka addabi al'umma a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum
  • Yan sanda sun cafke wani kasurgumin dan bindiga da ake nema ruwa a jallo mai suna Isiyaku Babangida a yayin samamen
  • Jami'an tsaron sun kuma kwato makamai da suka hada da bindigogin AK-47, alburusai da sauransu

Zamfara - Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta ce jami’anta sun kama wani Isiyaku Babangida, kasurgumin dan bindiga da ake nema ruwa a jallo.

Kakakin yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ne ya sanar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, jaridar The Cable ta rahoto.

Jami'an yan sanda
Yan Sanda Sun Kama Isiyaku Babangida, Kasurgumin Dan Bindigar Zamfara Da Ake Nema Ruwa A Jallo Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cewar Shehu, an kama Babangida ne a yayin wani aiki da jami’an tsaro suka gudanar a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da ke jihar.

Kara karanta wannan

Kananan Yara 3 Sun Mutu A Ginin Da Ya Rufta A Jigawar Tsada

Sanarwar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Jam’an yan sandan Zamfara, yayin da suke aikin fatrol, sun yi aiki kan wani bayanan sirri game da yunkurin da wasu guggun yan ta’adda karkashin shugabansu, Alhaji Bello ke yi na kai hari kan wasu garuruwa a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum.
“Nan take jami’an yan sandan suka shiga aiki sannan suka fasa kai mabuyar yan bindiga da ke kusa wanda ya kai ga yin musayar wuta a tsakanin yan fashin da yan sandan.
“Wutan da yan sandan suka bude ya sa sun yi nasarar daddake yan fashin, inda hakan ya tilasta masu tserewa da raunuka.
“An kama wani dan fashi da ake neman ruwa a jallo mai suna Isiyaku Babangida na kauyen Kabe da ke jihar Kebbi.”

Ya kara da cewa an kwato bindigogin AK-47, bindigogi na kira, da alburusai yayin samamen, Radio Nigeria Kaduna ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

Shehu ya kara da cewa:

“A yayin bincike, wanda ake zargin ya yi bayani kan yadda shi da sauran yan kungiyarsa masu bindigogin AK-47, suka farmaki kauyuka da dama a Anka, Bukkuyum, Gummi suka sace dabbobi sannan suka yi garkuwa da mutane da dama sannan suka tsare su har sai da yan uwansu suka biya kudin fansa.”

Yan Achaba Na Kwanciya Da Matanmu, Jami’an Yan Sanda Sun Yi Zanga-zanga

A wani labari na daban, mun ji cewa akalla jami’an yan sanda 480 ne suka gudanar da zanga-zanga kan zargin rashin biyansu albashin watanni 18 a Osun.

Sun yi tattaki a manyan unguwanni da mahadar Osogbo, babban birnin jihar Osun domin yin zanga-zanga, jaridar The Nation ta rahoto.

A watan Mayun 2021 ne aka rantsar da jami’an yan sandan a hedkwatar rundunar da ke jihar Osun bayan horar da su a watan Afrilun 2021. An kwashe su aiki ne don karfafa tsarin aikin rundunar ta hanyar bayar da bayanan sirri da sauransu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Buɗe Wa Jami'an 'Yan Sanda Wuta, Rayuka Sun Salwanta

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng