Hotunan Tinubu, Shettima da Gbajabiamila A Masallacin Juma'a Ya Dauki Hankulan Mutane

Hotunan Tinubu, Shettima da Gbajabiamila A Masallacin Juma'a Ya Dauki Hankulan Mutane

  • Kakakin majalisar tarayyar Najeriya, Honarabul Femi Gbajabiamila ya wallafa hotunansa tare da Bola Tinubu da Kashim Shettima a masallacin Juma'a a Facebook
  • Ma'abota amfani da shafukan sada zumunta sun rika bayyana mabanbantan ra'ayoyi game da hotunan wasu na yabo yayin da wasu kuma ku suka yi suka
  • A baya, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya gargadi takwararsa na Labour Party ya gargadi magoya bayansa kan yada labaran karya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressivs Congress, APC, Asiwaju Bola Tinubu, da abokin takararsa Kashim Shettima da Kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila sun yi sallar Juma'a tare a Abuja.

Hotunan Tinubu da Gbajabiamila da Kashim a masallacin Juma'a.
Hotunan Tinubu, Shettima da Gbajabiamila A Masallacin Juma'a Ya Dauki Hankulan Mutane. Hoto: Femi Gbajabiamila/Ayo Adeagbo
Asali: Facebook

Masallacin Juma'a
Hotunan Tinubu, Shettima da Gbajabiamila A Masallacin Juma'a Ya Dauki Hankulan Mutane. Hoto: Femi Gbajabiamila/Ayo Adeagba
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Wajibi Ne Mu Lashe Zaben 2023 Don Kada Mu Kare a Kotu, Shugaban APC

Masallaci
Hotunan Tinubu, Shettima da Gbajabiamila A Masallacin Juma'a Ya Dauki Hankulan Mutane. Hoto: Femi Gbajabiamila/Ayo Adeagba
Asali: Facebook

Da ya ke wallafa hotunan a shafinsa na Facebook, Gbajabiamila ya ce:

"Sallar Juma'a a masallacin Dantata, Abuja tare da dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar mataimakin shugaban kasa, Sen. Kashim Shettima da sauran masu ibada."

Ga wasu daga cikin abubuwan da masu amfani da intanet suka ce:

Ngene Charles C:

"Me yasa kullum a zaune ya ke".

Mahmud Kudu U:

"Barka da Juma'a kakakin majalisar mu."

Abdulaziz Mohammed:

"Amma kuskure ne sosai yadda suka bada tazara a sahu tsakanin kakakin da Bola Tinubu."

Mansur:

"Wai me yasa dan takarar ku ba ya iya tsayuwa yayin sallah?"

Algoni Goni Abuwa:

"Duk da cewa addu'a suke yi suna yin shi ne da girman kai. Babu hadda kafufuwa ma da kafada kamar yadda addini ya koyar."

Abba Ibrahim Tudunwada:

"Ayi kokari ana hade sahu yadda addini yace, Allah ya karbi ibadun mu."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yarima Charles, Ya Zama Sabon Sarkin Ingila, Ya Saki Jawabinsa Na Farko

Amos Adziba:

"APC ta rasa abin yin kamfen bayan hotunan ranar Juma'a."

Benefit AB Hill II

"Tambaya ta shine me yasa Tinubu ke zaune? Kuma idan amsar ka shine ba shi da lafiya, tambaya ta ta gaba shine shin wannan ne ke son zama shugaban kasa?"

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

A wani rahoton, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci takwararsa na Labour Party, Mr Peter Obi, ya ja kunnen magoya bayansa don su dena yada karya, makirci da aibanta shi da sauran yan takara.

Ya ce zaben kasar za ta yi armashi idan aka mayar da hankali wurin batutuwan da za su inganta rayuwar yan Najeriya da fito da su daga talauci a maimakon shirme irin na yan tasha wadanda ba su nufin kasar da alheri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164