Da Nine Buhari Zan Sauya Sunan Jami’ar Najeriya Ta Nsukka Zuwa Sunan Elizabeth, Inji Adamu Garba

Da Nine Buhari Zan Sauya Sunan Jami’ar Najeriya Ta Nsukka Zuwa Sunan Elizabeth, Inji Adamu Garba

  • Jigon jam'iyyar APC mai mulki ya yi kira ga dasa wani abin tunawa da sarauniyar Ingila Elizabeth da ta rasu jiya
  • Adamu Garba II ya ce idan da shine shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai sauya sunan jami'a sunan sarauniyar
  • A jiya ne duniya ta kadu da samun labarin mutuwar sarauniyar Ingila Elizabeth II, an nada danta a matsayin magani

An shawarci shugaban kasa Muhmmadu Buhari na Najeriya da ya sauya sunan jami'ar Nsukka (UNN) zuwa sunan marigayiya sarauniyar Ingila.

Wannan kira dai na fitowa ne daga bakin tsohon dan takarar shugaban kasa a APC, Adamu Garba II a yau Juma'a 9 ga watan Satumban 2022.

A wani rubutu da ya yi a Twitter, Adamu Garba ya ce kamata ya yi a ce gwamnatin Najeriya ta sauya sunan jami'ar UNN zuwa ta Sarauniya Elizabeth II.

Kara karanta wannan

Kayan duniya: Wasu kadarori masu ban al'ajabi da sarauniya Ingila ta mutu ya bar wa magajinta

Adamu Garba ya ba Buhari shawarin a sauya sunan jami'ar Najeriya
Da nine Buhari zan sauya sunan jami'ar Najeriya ta Nsukka zuwa sunan Ellizabeth, inji jigon APC | Hoto: @adamugarba
Asali: Twitter

A cewarsa, wannan ne hanya mafi sauki da za a ke tunawa da sarauniyar da irin ayyukanta kasancewarta sarauniya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake karin bayani, Adamu ya kuma ce idan da shine shugaban kasa, zai ba da hutun kwanaki uku domin jimamin mutuwar sarauniyar da ta fi kowane sarki jimawa a karagar mulki.

A rubutun nasa guda biyu a Twitter, ya ce:

"Domin ci gaba da tunawa da sarauniya Elizabeth, ya kamata mu sauya sunan jami'ar Najeriya ta Nsukka zuwa jami'ar sarauniya Elizabeth ta Najeriya tun da itace jami'ar farko a Najeriya.
"Idan nine shugaban Najeriya a yau, zan ayyana kwanaki uku na jimamin mutuwar sarauniya Elizabeth II ta kasar Ingila."

Shugaba Putin Ba Zai Halarci Jana’izar Sarauniya Elizabeth Ba, inji Dmitry Peskov

A wani labarin, shugaban Vladimir Putin na kasar Rasha bai yi shirin halartar jana'izar Sarauniya Elizabeth II ba, in ji mai magana da yawunsa Dmitry Peskov a wani taron manema labarai a yau Juma'a 9 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Shugaban wata kasa mai karfin iko ya ce ba zai halarci bikin bison sarauniyar Ingila ba

Duk da cewa Rasha na mutunta ta saboda hikimarta, shugaba Putin ba zai halarci bikin ba kamar yadda Peskov ya bayyanawa manema labarai, Punch ta ruwaito.

Rahotanni daga kasashen duniya da dama sun mika sakon ta'aziyya ga murnar nadin saraunta ga sabon sarkin Ingila Charles III. Allah ya yiwa sarauniyar Ingila Elizabeth II rasuwa a Balmoral Castle na Scotland, gidanta dake tsaunukan Scotland a yammacin jiya Alhamis 8 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel