Shugaba Putin Ba Zai Halarci Jana’izar Sarauniya Elizabeth Ba, inji Dmitry Peskov

Shugaba Putin Ba Zai Halarci Jana’izar Sarauniya Elizabeth Ba, inji Dmitry Peskov

  • Yayin da shugabannin kasashen duniya ke haba-haba da halartar bikin bison sarauniyar Ingila, shugaban Rasha ya yi bayani
  • Shugaban ya ce sam bai da shirin halartar bikin, duk da cewa kasarsa Rasha na mutunta matsyain sarauniya
  • A jiya Alhamis ne Allah ya karbi ran sarauniyar Ingila Elizabeth II bayan shafe shekaru 70 a kan karagar mulki

Kremlin, Rasha - Shugaban Vladimir Putin na kasar Rasha bai yi shirin halartar jana'izar Sarauniya Elizabeth II ba, in ji mai magana da yawunsa Dmitry Peskov a wani taron manema labarai a yau Juma'a 9 ga watan Satumba.

Duk da cewa Rasha na mutunta ta saboda hikimarta, shugaba Putin ba zai halarci bikin ba kamar yadda Peskov ya bayyanawa manema labarai, Punch ta ruwaito.

Shugaban Rasha ba zai halarci bison sarauniyar Ingila ba
Shugaba Putin ba zai halarci jana'izar Sarauniya Elizabeth ba - Kremlin | Hoto: punchng.com
Asali: Getty Images

Rahotanni daga kasashen duniya da dama sun mika sakon ta'aziyya ga murnar nadin saraunta ga sabon sarkin Ingila Charles III.

Kara karanta wannan

Kayan duniya: Wasu kadarori masu ban al'ajabi da sarauniya Ingila ta mutu ya bar wa magajinta

Allah ya yiwa sarauniyar Ingila Elizabeth II rasuwa a Balmoral Castle na Scotland, gidanta dake tsaunukan Scotland a yammacin jiya Alhamis 8 ga watan Satumba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Labarin mutuwar sarauniyar da fadar Buckingham ta sanar, ya ja hankalin shugabannin duniya kuma da dama sun yi tsokaci tare da bayyana jimaminsu, ciki har da shugaba Buhari na Najeriya.

Tuni aka dauke kambin sarautar Ingila zuwa kan Yarima Charles III jim kadan bayan sanar da rasuwar mahaifiyarsa.

Elizabeth II ta dale karagar mulki ne itama bayan rasuwar mahaifinta Sarki George VI a ranar 6 ga watan Fabrairun 1952, a lokacin tana da shekaru 25 kacal, rahoton Heritage Times.

Sarauniyar ta shafe shekaru 70 a karagar mulki, kuma ta shekara 96 a duniya kafin rai ya yi halinsa.

Sarauniyar Ingila, Elizabeth II Ta Kwanta Da, Ta Rasu Tana da Shekaru 96

Kara karanta wannan

Hotunan Atamfofin da 'Yan Najeriya Suka Fitar Matsayin Ankon Bikin Mutuwar Sarauniyar Ingila

A jiya kun ji cewa, mun samu labarin rasuwar sarauniyar Ingila Elizabeth II bayan 'yar gajeriyar rashin lafiya da aka sanar ta yi a yau Alhamis 8 ga watan Satumba.

Rahotanni daga majiyoyi sun shaida cewa, masarautar Ingila ta tashi bakin labarin jirkicewar lafiyar sarauniya, lamarin da yasa likitoci ke kai komo a kanta.

A wata sanarwar da masarautar ta Ingila ta fitar, an sanar da rasuwar sarauniyar da yammacin Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.