Gwamna Sanwo-Olu Na Legas Ya Yi Sabbin Nade-Nade a Gwamnatin Jiharsa
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, ya yi sabbin nade-nade 11 a ma’aikatan gwamnatin jihar ta Legas a yau Alhamis 8 ga watan Satumba.
Da yake tabbatar da nade-nade, shugaban ma’aikatan jihar Legas, Hakeem Muri-Okunola ya ce wadanda aka nadan an tsamo su ne cikin tsanaki da cancanta daga ma'aikatan jihar.
Muri-Okunola a cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ya ce gwamnan ya nada sabbin manyan sakatarorin dindindin guda biyu da sakatarorin dindindin guda tara.
Ya kuma ce an zabo ma'aikatan aka nada din ne daga cikin mutanen da suka cancanta, wanda hakan ya biyo bayan bin kwakwaf da tantancewar gwamnati cikin tsanaki
A cewar Muri-Okunola an yi gwajin tantance jami'an na gwamnati ne a watan Afrilun 2022. Ga jerin wadanda suka tsallake tantancewar gwamnati.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Manyan sakatarorin dindindin
- Osinaike Olusegun Olawale - Ma'aikatar ilimi (District IV)
- Oyetola Idowu Olufunke, - Ma'aikatar ilimi (District III)
Sakatarorin dindindin
3. Oyegbola Olasunkanmi Mopileola, tsohon daraktan harkar gudanarwa da da daukar ma'aikata a ofishin ayyukan gwamnati
4. Dawodu Kikelomo Arinola, tsohon daraktan kudi a ma'aikatar sufuri
5. Toriola Abdulhafis Gbolahan, tsohon daraktan harkar injiniyanci a ma'aikatar sufuri
6. Abidakun Olubusola Ajibola, tsohon daraktan gudanarwa da daukar ma'aikata a ma'aikatar lafiya.
7. Aina Ololade Olasupo, tsohuwar daraktar dudanarwa da daukar ma'aikata a ofishin assasawa da horarwa.
8. Kasunmu Ibilola Olufolake, tsohon babban manajan hukumar rijistar gidaje na jihar Legas
9. Sogunle Michael Olumide, tsohon daraktan hulda da jama'a a ma'aikatar watsa labarai
10: Sotire Oluwole Olumide, tsohon daraktan ayyuka a ma'aikatar gidaje
11. Obajomo Ibrahim Amodu, tsohon daraktan tsare-tsare a ma'aikatar tsare-tsaren tattalin arziki da kasafin kudi.
Majalisar Dokokin Jihar Neja Ta Tsige Shugaban Masu Rinjaye da Mataimakiyarsa
A wani labarin, a yau Alhamis 8 ga watan Satumba muke samun labarin cewa, 'yan majalisar dokokin jihar Neja sun karbe kujerar shugaban masu rinjaye, mataimakinsa da kuma shugaban masu tsawatarwa na majalisa.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, tuni 'yan majalisar suka zabo wadanda za su gaje su nan take, The Nation ta ruwaito.
Jami'an majalisar da aka tsige sune shugaban masu rinjaye Saleh Ibrahim, mataimakiyarsa Binta Mamman da shugaban masu tsawatarwa na majalisa Bello Ahmed.
Asali: Legit.ng