Majalisar Dokokin Jihar Neja Ta Tsige Shugaban Masu Rinjaye da Mataimakiyarsa

Majalisar Dokokin Jihar Neja Ta Tsige Shugaban Masu Rinjaye da Mataimakiyarsa

  • Majalisar dokokin jihar Neja ta tsige wasu shugabanni uku na majalisar bisa wasu dalilai, an maye gurbinsu
  • Rahoton da muke samu ya ce, an tsige su saboda sauke nauyin da aka daura musu kundin tsarin mulki
  • A shekarar nan an tsige shugabanni a majalisun dokokin jihohi daban-daban, ciki har da jihar ta Neja

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Neja - A yau Alhamis 8 ga watan Satumba muke samun labarin cewa, 'yan majalisar dokokin jihar Neja sun karbe kujerar shugaban masu rinjaye, mataimakinsa da kuma shugaban masu tsawatarwa na majalisa.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, tuni 'yan majalisar suka zabo wadanda za su gaje su nan take, The Nation ta ruwaito.

An tsige shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Neja
Da Dumi-Dumi: Majalisar Dokokin Jihar Neja Ta Tsige Shugaban Masu Rinjaye da Mataimakiyarsa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Jami'an majalisar da aka tsige sune shugaban masu rinjaye Saleh Ibrahim, mataimakiyarsa Binta Mamman da shugaban masu tsawatarwa na majalisa Bello Ahmed.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

An maye gurbinsu ne da Mohammed Abba Bala a matsayin shugaban masu rinjaye da Madaki Malik Bosso a matsayin mataimakinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, an ba Salihu Tama Edati shugaban masu tsawatarwa na majalisa.

Meye dalilin tsige su?

Wani sabon rahoton This Day ya yi karin haske game da tsige jami'an, inda yace ana zargin su da gaza sauke nauyin kudin tsarin mulki da aka daura musu a matsayinsu na shugabanni.

Rikicin tsige su ya fara ne yayin da dan majalisar dake wakiltar mazabar Edati Salihu Tama ya tada batu kan muhimmancin sauki hakkin aikin jama'a amma kakakin majalisar ya dakatar dashi.

Sai dai kakakin majalisa ya fahimta yayin da ‘yan majalisar suka jawo hankalinsa da cewa, batun da ya shafi al'umma bai bukatar katsewarsa ko ganin bukatar a rubuce.

Majalisar Zartaswar Jami’iyyar PDP Ta Amince Ayu Ya Ci Gaba da Shugabantar Jam’iyya

Kara karanta wannan

Allah-wadai: Rikici ya barke tsakanin Mali da Cote D'Ivoire, Buhari ya sha alwashin warwarewa

A wani labarin, wani rahoton Punch ya ce, majalisar zartaswar jam’iyyar PDP ta kasa ta amince Sanata Iyorchia Ayu ya ci gaba da shugabancin jam'iyyar.

Wannan na zuwa ne bayan majalisar ta NEC ta kada kuri'ar amince da Ayu, wanda hakan ke nufin shugaban jam’iyyar ba zai sauka daga mukaminsa a nan kusa ba.

Ana ci gaba da kai ruwa rana a jam'iyyar PDP game da shugabancin jam'iyyar, tun bayan barkewa rikici tsakanin gwamnan Ribas Wike da dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel