Kano: Yara 3 Sun Mutu Yayin Da Dakin Mahaifiyarsu Ya Rushe Ya Rufta Musu

Kano: Yara 3 Sun Mutu Yayin Da Dakin Mahaifiyarsu Ya Rushe Ya Rufta Musu

  • Wasu yara yan gida daya su uku sun riga mu gidan gaskiya a Kano sakamakon rushewar gini a gidansu a Kauyen Tarai
  • Saleh Jili shugaban hukumar bada agajin gaggawa na Jihar Kano, SEMA, ya jagoranci tawaga zuwa ta'aziyya tare da bawa iyalan kayan tallafi
  • Abubakar Usman, mahaifin yaran da suka rasu ya ce baya gari ya yi tafiya aka kira shi a waya aka sanar da shi cewa dakin matarsa ya rushe kuma yaransu uku sun rasu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - Wani abin bakin ciki ya faru a kauyen Tarai na karamar hukumar Kibiya a Kano bayan rushewar wani gini da ya yi sanadin rasuwar yara uku yan gida daya.

Mahaifin wadanda suka rasu, Abubakar Usman ya shaidawa babban sakataren SEMA, Saleh Jili lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa ta'aziyya a garin.

Kara karanta wannan

Yan Bindige Sun Yi Wa Yan Bijilante Kwanton Bauna, Sun Bindige 2 Har Lahira A Abuja

Taswirar Jihar Kano.
Wasu Yara 3 Yan Gida Daya A Kano Sun Rasu Bayan Gini Ya Rufta Musu A Gida. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce wadanda suka rasu suna Umar Abubakar, Aliyu Abubakar da yar uwarsu Aisha Abubakar, kamar yadda The Punch ta rahoto.

A cewar mahaifin, yaran yan shekara hudu, biyar da bakwai sun rasu ranar Lahadi 7 ga watan Agusta lokacin da ginin dakin mahaifiyarsu ya rufta saboda ruwan sama da aka yi na kwana biyu.

Ya ce:

"Wani dan uwa na ya kira ni ya sanar da ni cewa yaya na uku sun rasu domin na yi tafiya zuwa kasuwanci.
"A rana ta 17 an kira ni misalin karfe 6 na safe cewa daya daga cikin dakunan gida na ya rufta kuma ya yi sanadin rasuwar yara na ku," in ji mahaifin.

Martanin shugban SEMA

Shugaban SEMA, Saleh Jili, wanda ya jagoranci tawagar zuwa Kibiya ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi bakin cikin samun labarin mutuwar yaran, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ba gaskiya bane: Gwamna dan rashawa da Buhari ya yiwa afuwa ya musanta batun yin takara a 2023

Ya ce hukumar zata tattara rahoto ta bawa gwamnati don a dauki mataki.

Jili ya ce hukuma ta samar da katifu, matashi da kayan abinci da na gini ga iyalan wadanda suka rasun.

"Muna bada shawara a dena gini kan hanyar ruwa," in ji shi.

Hakimin Kibiya kuma Sarkin Shanun Rano, Alhaji Abubakar Ila, ya yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.

Kano: Mahaifi Da Dansa Sun Nutse A Cikin Rijiya Sun Mutu

A wani rahoton, wani mutum dan shekara 60 mai suna Malam Bala da dansa, Sanusi Bala, ɗan shekara 35 sun mutu a rijiya a Sabon Garin Bauchi, karamar hukumar Wudil na Jihar Kano a lokacin da suke yashe rijiyar.

Mai magana da yawun hukumar kwana kwana na jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa a ranar Laraba, rahoton Punch.

Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru a safiyar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya Shaidawa ‘Yanuwan Fasinjojin Jirgin da Aka Dauke Ya Bayyana

Asali: Legit.ng

Online view pixel