Wata karfen gada ta halaka akalla mutane 6 a garin Kaduna (Hotuna)

Wata karfen gada ta halaka akalla mutane 6 a garin Kaduna (Hotuna)

- Karfen gada ta kashe mutane 6 a unguwar Kawo da ke Kaduna

- Daya daga cikin wadanda suka rasa ransu har da wata daliban makaranta

- Mutun daya na cikin matsananciyar jinya

Karfen da aka kafa a gadar wucewar ababen hawa a babban titin da ke Kawo a garin Kaduna ta fado kan wata karamar motar fasinjoji a inda nan take ta kashe mutane 6 dake cikin motar yayin da ta bar daya cikin su a matsananciyar jinya.

Bayanai daga majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewa a cikin wadanda suka rasa ransu har da wata daliba dake kan hanyar zuwa zana jarabawar makaranta da ke yankin Rigachikum wanda ke gaban unguwar Kawo.

Karfen dai an sanya ta ne a farko da karshen gadar da nufin hana masu manyan motoci zirga-zirga ta saman gadar.

Wata karfen gada ta halaka akalla mutane 6 a garin Kaduna (Hotuna)
Karfen gadar da halaka mutane 6 a Kaduna

Legit.ng ta tattaro cewa, wannan lamarin dai ta faru ne a ranar Litinin, 18 ga watan Agusta.

Wata karfen gada ta halaka akalla mutane 6 a garin Kaduna (Hotuna)
Karfen gada da ke unguwar Kawo

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

KU KARANTA: Karfaffan direban mota ya bazar da wani Fasinja, ya zubar masa hakora

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng