Ana Batun Yajin ASUU, Jami’ar AUN a Adamawa Ta Dauki Sabbin Dalibai 3,000 Bana, Majiya Mai Tushe

Ana Batun Yajin ASUU, Jami’ar AUN a Adamawa Ta Dauki Sabbin Dalibai 3,000 Bana, Majiya Mai Tushe

  • Yayin da jami'o'in Najeriya ke garkame, jami'o'i masu zaman kansu a kasar nan na ci gaba da aiki tukuru
  • Jami'ar AUN dake birnin Yola a jihar Adamawa ta dauki sabbin dalibai da suka kai akalla 3000 a shekarar nan
  • Hakazalika, wata jami'a a jihar Jigawa ta dauki sabbin dalibai 130 a zangon shekarar nan kamar yadda rahoto ya bayyana

Adamawa - Jami’ar Amurka a Najeriya (AUN) dake Yola, ta ce ta dauki sabbin dalibai sama da 3,000 a tsangayoyi daban-daban da jami'ar ke dashi

Ya zuwa yanzu dai AUN ce jami'a mai zaman kanta daya tilo dake aiki a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, rahoton Daily Nigerian.

A bangare guda, Jami’ar Khadija Majiya (KUM) ce jami’a mai zaman kanta daya tilo a jihar Jigawa, wacce ke a garin Majia ta karamar hukumar Taura.

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

AUN na dauki sabbin dalibai 3000, KUM ta dauki 130 bana
Ana Batun Yajin ASUU, Jami’ar AUN a Adamawa Ta Dauki Sabbin Dalibai 3,000 Bana, Majiya Mai Tushe | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Jami'o'i biyun na aiki ne a Najeriya daidai da umarnin Hukumar Jami’ar Najeriya (NUC), kuma suna koyar da fannoni daban-daban na ilimi..

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban Daraktan Sadarwa na AUN, Daniel Okereke ya ce jami’ar daukar dalibai a ciki da wajen Najeriya.

Ya ce tsarin daukar sabbin dalibai a jami'ar na tafiya ne daidai da tsarin karatu a Amurka, kuma ana daukar dalibai sau biyu a shekara.

Tarihin AUN da ke rubuce a shafin Wikipedia ya ce, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ya kafa jami'ar a shekarar 2004, ta fara daukar dalibai a 2005.

Mun samu dalibai da yawa daga jami'o'in gwamnatin Najeriya

A cewar jami'in na AUN, jami'ar ta karbi dalibai da dama daga jami'o'in gwamnatin Najeriya kuma daga sassa daban-daban na kasar.

Duk da cewa jami'o'in Najeriya na garkame da sunan yajin aiki, Daniel ya ce sam yajin aikin ASUU bai da nasaba da karin dalibai da jami'ar ta samu.

Kara karanta wannan

Jerin Jami'o'i 10 Da Suka Bijirewa ASUU, Basu Shiga Yajin Aiki Ba

Ya kuma bayyana cewa, jami'ar daukar sabbin dalibai ne cikin tsanaki tare da duba da la'akari da irin kayayyakin da jami'ar ke dashi.

A bangaren jami'ar KUM ta Jigawa, jami'ar hulda da jama'a Salima Aminu ta ce an dauke sabbin dalibai 130 a shekarar nan, rahoton Pulse.

Ita ma ta ce sam batun ASUU bai shafi komai na kari ko ragin samun dalibai a jami'ar ba.

Kungiyar malaman jami'a sun shafe watanni sama da shida suna yajin aiki, lamarin da ya ajiye daliban kasar nan a gida na tsawon lokaci.

Bayan Kiran Dalibai, Jami’ar Gombe Ta Yi Watsi da ASUU, Ta Kira Malamai Su Dawo Aiki

A wani labarin, hukumar gudanarwar jami'ar jihar Gombe (GSU) ta kira dukkan malaman ta bukaci dukkam ma'aikatanta dake hutun karatu da su gaggauta dawowa aiki.

Wannan na zuwa kira na zuwa ne a yau Litinin 5 ga watan Satumba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jami'ar Arewa ta yi watsi da ASUU, ta ce malamai su gaggauta dawowa bakin aiki

Magatakardar jami’ar, Dakta Abubakar Aliyu Bafeto, a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan Satumba 5, 2022, ya umurci malaman jami'ar da ke karatu a Najeriya da su koma bakin aiki kasancewar jami'ar ta dawo karatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.