Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haream 200 Da Manyan Kwamandoji 5

Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haream 200 Da Manyan Kwamandoji 5

  • Rundunar sojojin Najeriya sun yi gagarumin nasara a kan mayakan kungiyar Boko Haram
  • Dakarun sojojin sama na Operation Hadin Kai sun yi ruwan bama-bamai kan mayakan inda suka kashe mutum 200 da manyan kwamandoji biyar
  • Kwamandojin da aka kashe sun hada da Abou Hauwa, (Munzir) Amir Shettima, Akura Buri(Nakif), Abou Zainab, Abou Idris

Borno - Mayakan Boko Haram sun sha kashi a hannun dakarun sojojin Operation Hadin Kai inda suka halaka mayakan kungiyar guda 200 ciki harda manyan kwamandojinsu guda biyar a jihar Borno, The Cable ta rahoto

Dakarun sojojin sama da suka hada da bataliya ta 199 da ta 222 sun kaddamar da hare-haren ne a ranar 1 ga watan Satumban 2022.

Jiragen yaki
Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haream 200 Da Manyan Kwamandoji 5 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sojojin sun yi ruwan bama-bamai a mabuyar yan ta’addan a Gaizuwa wanda aka fi sani da Gabchari, Sheruri, Mantari da Mallum Masari, kauyukan karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Hotunan: Haifaffiyar Jihar Kano Ta Zama Lauya A Manyan Kotunan Ingila Da Wales

Wani jami’in leken asiri ya fada ma Zagazola Makama, masanin harkar tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa wani bincike da aka gudanar ya tabbatar da harin ya yi sanadiyar kashe manyan kwamandojin Boko Haram.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamandojin da aka kashe sun hada da Abou Hauwa, (Munzir) Amir Shettima, Akura Buri(Nakif), Abou Zainab, Abou Idris da mayakansu, rahoton PM News.

Majiyoyin sun bayyana cewa a yayin farmakin dakarun sojin kasa sun farmaki mabuyar yan ta’addan a Gafchari, inda suka yi musayar wuta da su lamarin da ya yi sanadiyar kashe fiye da mayaka 30 yayin da suran suka tsere da raunuka.

Rahoton ya kuma kawo cewa Rundunar sojin sama tare da hadin gwiwar dakarun sojin kasa, ta tura jiragen yaki biyu don farmakar yan ta’addan wanda ya yi sanadiyar kashe karin yan ta’adda 70.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Ta Kama 'Yahoo Boys' 41 Da Dukiyoyin Da Suka Mallaka

An kuma bayyana cewa wasu da dama da suka yi kokarin guduwa sun nitse a ruwa.

Har ila yau, ya ce an kaddamar da hari makamancin wannan a Sheruri lokacin da jirgin yaki ya kara ruwan bama-bamai a wani wurin mayakan da aka tura don su kai kautan bauna kan sojin kasa.

Ya ce jiragen yakin sun yi ruwan bama-bamai inda suka kashe kwamandoji biyu; Akura Buri (Nakif) da Abou Hauwa da mayakansu fiye da 63.

A cewarsa, yan ta’adda kadan da suka tsira a harin sojojin sun dawo a ranar 3 ga watan Satumba don tattara gawarwakin mayakansu a Sheruri da Gabchari.

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

A wani labarin, akalla mutum hudu ne suka mutu ciki harda babban limamin Gima, sannan wasu da dama sun jikkata yayin da mayakan Boko Haram suka farmaki garin Ngulde da ke karamar hukumar Askira-Uba ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka Yan Ta'addan Boko Haram 49

Mayakan sun kuma sace dabbobi da kayan abinci ba tare da cikas ba, bayan sun cinnawa motoci biyu wuta, kasancewar Ngulde garin manoma ne da ke a wani bangare na dajin Sambisa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa yan ta’addan da yawansu ya fi 20 dauke da Muggan makamai da bindigogi sun farmaki garin ne tun a ranar Juma’a sannan suka yi barna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel