Pantami: Yadda Na Shawo Kan Buhari, Aka Fasa Kara Farashin Yin Waya da Sayen Data
- Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi bakin kokarinsa wajen ganin ba a kara farashin yin waya da hawa yanar gizo ba
- Ministar sadarwa da tattalin arziki na zamanin yace takarda ya aikawa shugaban kasa, yana mai yi masa korafi
- Pantami yace tsadar amfani da wayoyin salula da yanar gizo yana da mummunan tasiri da illa ga tattalin arziki
Abuja - Ministar sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami yayi bayanin rawar da ya taka wajen ganin an dakatar da karin kudin yin waya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Isa Ali Ibrahim Pantami yana bayanin yadda takardar da ya rubutawa shugaba Muhammadu Buhari ta sa gwamnati ta canza matsaya.
Ministan ya yi wani zama da kwamitin shugaban kasa da ke kula da harkar harajin kamfanonin sadarwa a garin Abuja a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba 2022.
A cewar Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, ya aika korafi ga shugaban kasa, yana bayanin yadda karin kudin wayan zai jefa mutanen Najeriya a karin halin ha’ula’i.
Ba na goyon bayan wannan - Pantami
“Kwanan nan aka bada sanarwa cewa jami’an gwamnati sun fara kokarin shigo da haraji a cikin harkar sadarwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bisa tsarin mulkin Najeriya, kuma a matsayin wakilin shugaban kasa a wannan bangare, ban amince da haka ba.
Nayi wa shugaba Muhammadu Buhari bayani a wasikata wanda ta zama kamar korafi, nace ba mu goyon bayan haka.”
Amfani da Data ya zama tamkar dole
An rahoto Isa Ali Pantami yana cewa ana lafta haraji ne a kan kaya irinsu giya da sugari, yace makasudin hakan shi ne domin mutane su rage amfani da su a kasa.
A game da batun sayen data na hawa yanar gizo, Ministan yace sun shiga bangaren abubuwa masu muhimmanci, domin ana amfani da su wajen karatu da kasuwanci.
“Idan muka shigo da haraji, hakan yana nufin kashewa al’umma kwarin gwiwar amfani da kafofin sadawar zamani; kira, koyon karatu da kasuwancin yanar gizo.
Nayi wa Buhari bayanin yadda wadannan suka zama larura, duba da halin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu, bai kamata a kara cusa mutane a cikin wata wahala ba.”
Vanguard tace Ministan ya nunawa Buhari yadda lafta kudin zai kawo matsala ga tattalin arziki, domin harajin da ake karba a bangaren sadarwa ya yi yawa sosai.
Pantami ya samu karin matsayi
Kwanaki kun ji labari Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin kasar ya samu lambar zama ‘dan kungiyar Chartered Institute of Information Security.
Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya samu shaidar CIISec bayan yi masa jarrabawowi. Pantami ne mutumin farko a Afrika da ya samu wannan dama a Duniya.
Asali: Legit.ng