Abba Kyari Ya Magantu Kan Kadarori 14 Da FG Ta Bankado A Matsayin Nasa
- DCP Abba Kyari ya nesanta kansa da wasu kadarori guda 14 da ake zargin gwamnatin tarayya ta bankado a matsayin mallakinsa
- Gwamnatin Tarayya dai tana zargin Kyari yana da wasu gidaje, shaguna da kadarori da ba a san da su ba
- Dakataccen shugaban na IRT ya ce naira miliyan 2.8 da wani N200,000 ne kacal da shi a cikin asusunsa na banki
Abuja - Dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP Abba Kyari, ya karyata batun mallakar kadarori 14 da ake zargin gwamnatin tarayya ta bankado.
Kyari ya ce sabanin rahoton cewa an gano makudan kudade a asusun bankinsa, naira miliyan 2.8 ne kacal a asusunsa na UBA da kuma wani N200,000 a asusunsa na Sterling, jaridar Leadership ta rahoto.
A cewar wata sanarwa daga lauyansa, Barista Hamza Dan Tani, duk zarge-zargen da NDLEA ke yi dangane da kudade da kadarori mallakar Abba Kyari karya ne.
Dan Tani ya kuma bayyana cewa hukumar na batar da jama’a ne kawai don su yarda cewa dukiyoyin na Abba Kyari ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma bayyana cewa yan kasuwar da suka mallaki wadannan kadarorin sannan suka bayar da takardunsu sun rigada sun shigar da hukumar NDLEA kara a babbar kotun tarayya na Maiduguri, Vanguard ta rahoto.
Wani bangare na jawabin ya ce:
“An janyo hankalinmu zuwa ga wata wallafar karya a wasu sashin kafofin watsa labarai a ranar Litinin, 5 ga wata inda a jaridun aka ce gwamnatin tarayya ta bankado wasu kadarori 14 da suka hada da shaguna, gidaje, wurin wasan folo, filaye da gonaki mallakin tsohon kwamandan IRT, Abba Kyari, wanda ya kasance mataimakin kwamishinan yan sanda.
“Muna son sanar da al’umma gaskiyar magana kai tsaye. Shari’ar da NDLEA ke yi a kotu kan Abba Kyari da wasu hudu bata yi masu dadi ba. Suna tsammanin shari’ar kotun zai tafi daidai tare da nasara a bangarensu kamar yadda shari’ar kafar labarai da suka dauki nauyi ya yadu a tsakanin Fabrairu da Afrilun 2022. Sun gaza fahimtar cewa sabanin shari’ar midiya kotu na bukatar ainahin hujjoji na hakika wanda NDLEA bata da su a wannan shari’ar."
Ya ci gaba da cewa hukumar NDLEA na kokarin ganin ta bata sunan Abba Kyari ta kowani hali saboda sun san kokarinsu na baya ya gaza domin har yanzu yawancin yan Najeriya da ke son zaman lafiya suna bayansa duk da tuggun da suka shirya masa.
Ya kara da cewa:
“NDLEA ta sake daukar nauyin wasu karairayi, labaran kanzon kurege, da zarge-zarge, sannan ta kara shigar da tuhumar karya kan Abba Kyari a kotu ba tare da hujja ba."
An Bankado Wasu Dukiyoyin Abba Kyari, An Sake Kai Shi Kotu da Zargin Laifuffuka 24
A baya mun ji cewa gwamnatin tarayya ta gano wasu kadarori 14 wanda ake zargin Abba Kyari ya mallaka. Tun tuni dai ake shari’a da babban jami’in ‘dan sandan.
Punch ta fitar da rahoto cewa binciken gwamnatin Najeriya ya gano akwai katafaren shaguna, rukunin gidaje da wani filin folo da Abba Kyari ya mallaka.
Haka zalika an gano wasu filaye da gidaje a hannun tsohon shugaban na dakarn IRT na kasa.
Asali: Legit.ng