Bayan Mijinta Ya Dankara Mata Saki, Mata Ta Tubure, Ta Ki Barin Gidansa
- Wani batu ya ba da mamaki yayin da mata ta ki barin gidan tsohon mijinta bayan da ya sake ba saboda wasu dalilai
- Miji ya yi bayani, hakazalika matar, inda kowa ya bayyana abin da ke masa ciwo da kuma dalilin neman hakkinsa
- Saki da rigimar aure na daya daga cikin abin da alkalai ke yawan samu, musamman a Arewacin Najeriya
Jihar Kaduna - Hassam Jimoh, wani magidanci dan shekara 55, Hassan Jimoh, ya nemi kotu ta kori matarsa Silifat Salawuddeen daga gidansa bayan ya sake ta, Daily Nigerian ta ruwaito.
Ya bayyana wannan roko ne a ranar Litinin 5 ga watan Satumba a wata kotun shari'a dake zamanta a Magajin Gari a jihar Kaduna, inda ya ba da labarin abin da ya faru.
Malam Jimoh da ya shigar da kara, ya roki kotu da ta amince masa da batun raba aurensa da Silifat saboda rashin jituwar dake tsakaninsu da ba za ta warwaru ba.
A cewarsa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A bazawara na aure ta. Mun shafe shekaru biyar tare amma a yanzu na gaji saboda babu dadin soyayya da ma zaman lafiya.
“Ta kwaso ‘ya’yanta daga inda ta baro zuwa gidana. Na nemi ta maida su gidan mahaifinsu amma ta ki.”
Malam Jimoh ya kuma shaida wa kotun cewa ya ba matar tasa kudi Naira 50,000 domin ta tattara kayanta ta kama hayar wani gida a wani wurin, amma duk da haka ta ki tafiya.
Na biya bashi da kudin da ya bani - Silifat ga kotu
Da take kare kanta, Silifat, ta fada wa kotun cewa ta ki barin gidan nasa ne saboda N50,000 da ba ta bai bai kai ga kama haya ba.
A kalamanta:
“Na kashe kudin da ya bani wajen warware basukan da ke kaina na kayan abinci da karba."
"Mijina bai kafe kan hakkinsa na ciyar da iyali ba har na tsawon watanni hudu."
Mai shari'a Rilwanu Kyaudai, ya dage ci gaba da sauraran karar zuwa ranar 14 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan ko ya amince da bukatar Malam Jimoh na korar matar ko a'a.
'Karar Neman Saki: 'Dama Ba Aure Kuka Yi Ba', Zaman Dadiro Ku Kayi Na Shekaru 27, Kotu Ga Wasu Masoya
A wani labarin, wata kotun kwastamari a Ibadan ta fada wa wasu masoya, Olanrewaju da Fatima, da ke neman saki cewa dama zaman da suka yi tare na shekara 27 ba aure bane don ba a biya sadaki ba.
Da ya ke yanke hukunci, shugaban kotun, S.M. Akintayo ya ce dokar gargajiya da al'ada a Najeriya ta bukaci a biya sadaki ga iyayen yarinya kafin a tabbatar da aure.
Ta ambaci sassa da dama na doka, Akintayo ta ƙarƙare cewa babu aure tsakaninsu ballantana a yi maganan saki saboda rashin biyan sadakin kamar yadda NAN ta rahoto.
Asali: Legit.ng