'Karar Neman Saki: 'Dama Ba Aure Kuka Yi Ba', Zaman Dadiro Ku Kayi Na Shekaru 27, Kotu Ga Wasu Masoya

'Karar Neman Saki: 'Dama Ba Aure Kuka Yi Ba', Zaman Dadiro Ku Kayi Na Shekaru 27, Kotu Ga Wasu Masoya

  • Wata kotun majistare ta yi watsi da wani karar da wani mutum ya shigar na datse aurensa da masoyiyarsa Fatima
  • Kotun ta bayyana cewa babu batun saki duba da cewa zaman dadiro kawai suka yi na shekaru 27 tunda ba a biya sadakin aure ba
  • Duk da haka, kotun ta umurci Fatima ta nesanci mahaifin yayanta Adeniran wanda ya yi korafin cewa ta cika rigima da rikici don haka ya ke son su rabu

Ibadan - Wata kotun kwastamari a Ibadan ta fada wa wasu masoya, Olanrewaju da Fatima, da ke neman saki cewa dama zaman da suka yi tare na shekara 27 ba aure bane don ba a biya sadaki ba.

Da ya ke yanke hukunci, shugaban kotun, S.M. Akintayo ya ce dokar gargajiya da al'ada a Najeriya ta bukaci a biya sadaki ga iyayen yarinya kafin a tabbatar da aure.

Kara karanta wannan

An Rotsa Wa Wani Kai Da Kwalban Giya a Mashaya Ya Mutu a Bayelsa

'Karar Neman Saki: 'Dama Ba Aure Kuka Yi Ba', Zaman Dadiro Ku Kayi Na Shekaru 27, Kotu Ga Wasu Masoya
Neman Saki: 'Dama Ba Aure Kuka Yi Ba', Zaman Dadiro Ku Kayi Na Shekaru 27, Kotu Ga Wasu Masoya. Hoto: @nannews_ng.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ambaci sassa da dama na doka, Akintayo ta ƙarƙare cewa babu aure tsakaninsu ballantana a yi maganan saki saboda rashin biyan sadakin kamar yadda NAN ta rahoto.

Ta kuma ce ba a yi wasu abubuwa masu muhimmanci ba kafin a ce Fatima ta zama matar Adeniran.

"Kawai don mahaifin Fatima ya tambaya idan tana son Adeniran bai gamsar a al'adance cewa sun yi aure ba.
"Kuskure ne a yi tsammanin cewa idan an haifi yaro ko yara shi kenan mace da namiji sun zama mata da miji.
"A'a, babu aure a tsakanin su, kawai zama tare suke yi, kawai suna zama tare ne a gida ɗaya," in ji Mrs Akintayo.

Kotun ta kuma yanke hukuncin cewa Fatima ta dena damu, cin mutuncin da yi wa Adeniran barazana daga yau.

Kara karanta wannan

Ya zama na Hajiya: Mai neman aiki ya fada tarkon son shugabarsa, itama tayi caraf da abun ta

Adeniran ya nemi a raba shi da Fatima saboda wasu halayenta

Da farko, Adeniran, ma'aikacin gwamnati mai ritaya mazaunin Molade a Ibadan ya yi bayanin cewa Fatima ta cika neman rikici da magiya, News Wire NGR ta rahoto.

Mr Adeniran ya ce sau takwas ana tsare ta sakamakon masifarta da fada da surukai, yan haya da makwabta a gari.

Ya ce har dan uwansa da ya taba basu wurin zama kafin su gina gidansu ya gaji ya kore su saboda halin Fatima.

"Fatima bata yarda in taɓa ta yanzu, tana yawan cewa ina wari.
"Kuma tana lalata kayan wutan lantarki na gida da zarar ranta ya ɓaci.
"Ta saba zargin cewa ina bin matan banza," mai shigar da karar ya fada wa kotu."

Martanin Fatima a kotu

A bangarenta, Fatima, yar kasuwa ta roki kotun kada ta kawo karshen soyayyar su.

Amma, ta ce mijinta mutum ne mai yawan shiga al'umma kuma yana yawan bin mata.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC su na tunanin mikawa Buhari sunayen mutum 2, sai ya zabi Magajinsa

"Adeniran yana da akalla ƴan mata takwas kuma wasu daga cikinsu har suna zuwa su kawo min kyauta idan na haihu ana bikin suna.
"Har ta kai ga wani lokaci da Adeniran ke faɗa min cewa yana son ƙara aure," matar ta fada wa kotu.

Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa

A wani labarin daban, wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.

Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel