Babu Wata Barazana Game da Faruwar Babban Zaben 2023, Inji IGP Alkali Baba
- Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya ya magantu kan barazanar tsaro a zabukan 2023 mai zuwa nan kusa
- A wani jawabin da IGP Alkali Usman Baba ya yi, ya ce babu wata matsala, kuma tabbas zaben ba zai zo da tasgaro ba
- 'Yan Najeriya da kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun damu matuka kan yadda lamurran tsaro ga kuma zabe na zuwa
Amurka - Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, yayin da zaben 2023 ke kara karatowa, Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Baba, ya yi tsokaci game da faruwar zaben, inda yace sam babu wata barazana, za a gudanar da zaben 2023.
Shugaban na 'yan sanda ya yi wannan tsokaci ne a wata sanarwa da Olumuyiwa Adejobi, jami’in hulda da jama’a na rundunar, ya fitar ranar Lahadi 4 ga watan Satumba a Abuja.
A cewar Alkali, ya ba da tabbacin babu matsala ne biyo bayan nazari da cikakken bincike kan barazanar da rundunar ta yi.
Rahoton Premium Times ya ce, Alkali ya yi wannan tsokaci ne a wata ganawa da Todd Robinson, mataimakin sakatare na ofishin kula da harkokin muggan kwayoyi a ma'aikatar harkokin wajen Amurka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkali ya gana da jami’in na Amurka ne a taron shugabannin ‘yan sanda na Majalisar Dinkin Duniya, wanda aka gudanar a kasar ta Amurka.
Manufar taron da Alkali ya halarta
A cewar sanarwar, tattaunawar ta mai da hankali ne ga yadda za a inganta tallafi ga shirin horar da ‘yan sandan Najeriya.
Hakazalika, Alkali ya ce an fi mayar da hankali ne musamman kan horar da rundunonin dubaru ke aiki yankin Arewa maso Gabas da sauran wurare na musamman a fadin Najeriya.
Ya kara da cewa, tattaunawar ta kuma duba bukatar sanin yiwuwar zabeukan 2023 da za a yi a shiyyoyin siyasa shida na fadin kasar
A bangare guda, taron ya kuma duba tare da tattaunawa kan batun horas da ‘yan sanda fannin batutuwan aikin zamani kamar binciken kwakwaf, hulda da jama'a da tsaron yanar gizo.
A nasa jawabin, Mista Robinson ya yabawa ‘yan sandan Najeriya kan aiki tukuru da kuma irin nasarorin da shugabancin rundunar ke samu.
Manyan alkawura 3 da IGP Baba ya daukar wa ‘yan Najeriya bayan kama aiki
A wani labarin, ko tantama babu, sabon Sufeto-Janar na 'yan sanda (IGP) Usman Alkali Baba, ya hau kujerar shugabanci ne a lokacin da yake akwai alamun tambaya da yawa tattare da tsarin tsaron Najeriya.
Tsawon shekaru da dama, 'yan ƙasar sun yanke kauna da rundunar yan sanda, sannan kuma saboda dalilai masu ma'ana, koyaushe suna shakkar karfin ikon 'yan sanda wajen rage matsalar rashin tsaro.
Sai dai kuma, IGP Baba a ranar Laraba, 7 ga Afrilu, yayi wasu maganganu na fatar baki don dawo da martabar rundunar.
Asali: Legit.ng