Manyan alkawura 3 da IGP Baba ya daukar wa ‘yan Najeriya bayan kama aiki

Manyan alkawura 3 da IGP Baba ya daukar wa ‘yan Najeriya bayan kama aiki

Ko tantama babu, sabon Sufeto-Janar na 'yan sanda (IGP) Usman Alkali Baba, ya hau kujerar shugabanci ne a lokacin da yake akwai alamun tambaya da yawa tattare da tsarin tsaron Najeriya.

Tsawon shekaru da dama, 'yan ƙasar sun yanke kauna da rundunar yan sanda, sannan kuma saboda dalilai masu ma'ana, koyaushe suna shakkar karfin ikon 'yan sanda wajen rage matsalar rashin tsaro.

Sai dai kuma, IGP Baba a ranar Laraba, 7 ga Afrilu, yayi wasu maganganu na fatar baki don dawo da martabar rundunar.

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Buhari bai halarci taron kaddamar da littafin uwar gidansa Aisha ba

Manyan alkawura 3 da IGP Baba ya daukar wa ‘yan Najeriya bayan kama aiki
Manyan alkawura 3 da IGP Baba ya daukar wa ‘yan Najeriya bayan kama aiki Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

Sabon shugaban ‘yan sandan ya yi alkawura da dama na sakewa da karfafa rundunar yan sandan Najeriya a daidai lokacin da satar mutane, kisan rashin tunani, da duk wasu nau’ikan aikata laifuka ke addabar kasar.

1. 'Yan sandan jiha

A wani rahoto da jaridar Tribune ta wallafa, shugaban 'yan sandan ya tabbatarwa da' yan kasar cewa wa'adinsa zai ba da fifiko wajen kafa yan sandan jiha a matsayin babbar dabarar yaki da kawar da ta'addanci.

Da yake bayyana cewa zai ci gaba daga inda wanda ya gada ya tsaya, Baba ya ce:

“Za mu ci gaba da aiki da shi. Wanda ya gabace ni ya tafi muna a wani mataki na fari, mun fara shi amma ba mu yi nisa ba, saboda haka, duk hanyoyin an tsara su kuma za mu ci gaba da shi tare da hadin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki."

2. Inganta yanayin tsaro

IGP din ya ce za a samu ci gaba abin yabawa a yanayin tsaron Najeriya don haka, ya yi kira ga kowa da kowa da su taimaka wa ‘yan sanda yayin da suke tunkarar miyagun laifuka a karkashin jagoranci na hakika.

Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zai sa fashi da makami da ta’addanci su zama tarihi a cikin kasar.

KU KARANTA KUMA: 2023: Daga karshe Arewa ta bayyana matsayinta akan zaben shugaban kasa, tayi watsi da tasirin addini

3. Sauyi a tsarin aiki

IGP Baba ya bayyana cewa za a samu gagarumin sauyi a tsarin gudanar da ayyukan rundunar wajen magance rashin tsaro a fadin kasar.

A wani rahoto daga jaridar Punch, ya kaddamar da cewa:

“Na kuma sami kwarin gwiwa da cewa IGP mai barin gado ya kafa tushe mai kyau kuma ya kuma kafa al'adar kwararru a rundunar.

"Wadannan za su kara min kwarin gwiwa a matsayina na sabon IGP mai rikon kwarya, don karfafa dabarunmu da samar da abin da ake bukata na shugabanci da zai sauya labaran dangane da dabarun gudanar da ayyukanmu game da barazanar da tsaro ke fuskanta a yanzu."

A wani labarin, mun ji cewa mutane na zaman dar-dar sakamakon jin karar harbe-harben bindiga a garin Aba da ke jihar Abia a kusa da inda ofishin yan sanda ya ke.

Mazauna garin suna gudanar da harkokinsu da suka saba kwatsam sai jami'an tsaro suka fara harbe-harbe da bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An rufe dukkan hanyoyin da za su bulla da mutane zuwa unguwar da ofishin yan sandan ya ke an kuma umurci mutane su koma gidajensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel