Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Zuba Wadanda Suka Sace a Masallacin Juma'a a Gonakinsu

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Zuba Wadanda Suka Sace a Masallacin Juma'a a Gonakinsu

  • 'Yan bindigan da suka kai hari Masallacin Juma'a tare da sace mutane 44 sun zuba su a gonakinsu inda suke musu aiki
  • Kamar yadda 'yan bindigan suka sanar da iyalan wadanda suka sace, geronsu da dawarsu ta isa girbi, shi suke musu a halin yanzu
  • 'Yan uwan wadanda lamarin ya ritsa da su sun ce har yanzu 'yan bindiga basu bukaci kudin fansa ba daga wurinsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Masallata 44 da 'yan bindiga suka sace daga Masallacin Juma'a a Zamfara suna gonakin 'yan bindigan inda suka zuba su suna musu noma, Daily Trust ta gano hakan.

Zamfara Bandits
Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Zuba Wadanda Suka Sace a Masallacin Juma'a a Gonakinsu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mazaunan yankin sun sanar da Daily Trust cewa, 'yan bindigan sun kira 'yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su tare da sanar musu cewa suna hannunsu amma suna aiki a gonakinsu na hatsi, har yanzu dai basu yi maganar kudin fansa ba.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Ta'adda Sun kai Sabon Farmaki Abuja, Sun Tafka Mummunar Ta'asa

"Gonakinmu na gero sun isa girbi kuma wadanda muka yi garkuwa da su suna mana aiki,"

- Daya daga cikin 'yan bindigan ya sanar kamar yadda wani Abubakar Bukkuyum ya bayyana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar Juma'a da gabata, 'yan bindiga sun kwashe mutane masu tarin yawa daga babban Masallacin Juma'a na Zugu dake karamar Hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan sun boye makamansu a kaya kuma suka tsinkayi Masallacin inda Liman ke dab da fara huduba. Sun bukaci na farfajiyar Masallacin da su shiga ciki.

Wani ganau ya bayyana cewa:

"Babu wanda ya ga bindugun kuma mutane da yawa sun yi kuskuren musu kallon masu bauta, babu wanda ya maida hankali wurinsu saboda a boye bindigunsu suke.
“Sai dai, bayan sun shiga cikin Masallacin, sun fitar da bindigun tare da yin harbin jan kunne."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kwashe Matafiya 32 Dake Dawowa Daga Jana'iza a Ondo

"Sun tarkata masu sallar zuwa cikin daji amma wasu sun arce, liman ya sha da kyar amma ladan an tafi da shi.
"Sun kara da hadawa da wasu dake farfajiyar masallacin inda suka yi garkuwa da su." ya kara da cewa.

A yayin da aka tuntubi kakakin frundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, yace suna cigaba da nema tare da kokarin ceto wadanda aka sace.

Katsina: 'Yan Bindiga Sace Mata Masu Juna 2, da Mutum 13 a Sabon Hari

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun kutsa yankin Low Cost dake Dutsen Reme a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina inda suka sace mutum hudu.

Wannan lamarin na zuwa ne kamar yadda mazauna yankin suka ce wurin karfe 10 na dare Juma'a, Daily Trust ta rahoto.

Kamar yadda wani Ahmed Ridwan, mazaunin Dutsen Reme ta bayyana, maharan sun yi amfani da ruwan saman da ake yi inda suka ci karensu babu babbaka.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Asali: Legit.ng

Online view pixel