Yadda Rashin Tsaro Ya Jawo Aka Rufe Makarantu Fiye da 600 a Jihohin Najeriya
- Ana kiyasin cewa akwai makarantu kusan 615 a Najeriya da an daina karantarwa a halin yanzu saboda tabarbarewar tsaro
- A jihohin Arewa da-dama, hukumomi sun tsaida karantarwa a wasu makarantu a dalilin rashin tsaro da ake fama da shi
- Wannan lamarin ya shafi jihohi irinsu Kaduna, Zamfara, da irinsu Neja tun da ‘yan ta’dda suka rika awon gaba da yara
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Nigeria - Wani dogon rahoto da ya fito daga jaridar nan ta Punch, ya nuna cewa akwai makarantu kimanin 615 da ke rufe a halin yanzu a Najeriya.
Matsalar tsaro da ake fama da ita a jihohi da dama yayi sanadiyyar rufe wadannan makarantu. Lamarin ya ta’azzara a yankin Arewacin kasar nan.
A ‘yan shekarun bayan nan, ‘yan ta’adda sun rika kai farmaki a yankunan Kaduna, Zamfara, Katsina da Neja, har da Sokoto, Kebbi, da dai sauransu.
Tsakanin 2014 zuwa yanzu, ‘yan ta’adda sun yi awon gaba da dalibai fiye da 1000. Abin farin cikin shi ne an yi nasarar gano mafi yawa a cikinsu.
Yadda jihohi suke fama a yau
Rahoton yace a kudancin Kaduna abin ya yi kamari, domin lamarin ya shafi makarantu fiye da 500. An rufe makarantun yankin ko an kai masu hari.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Makarantun da matsalar tsaro ta shafa a Zamfara sun zarce 100, yanzu duk an rufe su. Abin ya kai wasu makarantun sun zama mafakar wasu ‘yan bindiga.
Shugaban SUBEB na Zamfara, Kabiru Attahiru yace an rufe makarantu kimanin 75 zuwa yanzu. Mafi yawan makarantun da aka addaba na 'yan mata ne.
A jihohi irinsu Adamawa, malamai da dalibai duk suna cikin dar-dar. Shugaban NUT na jihar, Rodney Nathan yace babbar matsalar ita ce rashin katangu.
‘Yan bindiga sun addabi Benuwai, sai da aka rufe wasu makarantu. A irinsu Sokoto, an dunkule makarantu a wuri daya ne domin a samu zaman lafiya.
The Cable tace makarantu kusan tara aka rufe a Neja, an daina yin karatu. A Katsina, ba a rufe makaranta ko daya ba, sai dai ana ta fuskantar barazana.
Sace yaran makaranta
Mafi shaharar satar yaran da aka yi a makarantun Najeriya sun hada da 300 daga Chibok a 2014, 300 daga Damasak a Borno, 110 daga Dapchi a Yobe.
Idan za a tuna, an dauke yara 344 daga Kankara a Katsina, 276 daga Jangebe a Zamfara, 140 daga Chikun a Kaduna, sai kuma 102 daga Yauri a Kebbi.
Legit.ng Hausa za ta iya tuna ‘yan ta’adda sun kai hari a manyan makarantun gaba da sakandare irinsu jami’ar Greenfield da makarantar gandu a Afaka.
Asali: Legit.ng