Jami'ar GreenField: Masu garkuwa sun nemi Naira miliyan 800 kuɗin fansar ɗaliban Kaduna

Jami'ar GreenField: Masu garkuwa sun nemi Naira miliyan 800 kuɗin fansar ɗaliban Kaduna

- Masu garkuwa da suka sace dalibai a Jami'ar Greenfield a Kaduna sun nemi kudin fansa

- Yar uwan daya daga cikin daliban ta ce masu garkuwar sun ce a biya su Naira miliyan 800

- A cewarta, sun fara azabtar da daliban sun kuma ce za su halaka su duka idan ba a biya kudin fansar ba

Daya daga cikin iyalan daliban Jami'ar Greenfield da ke Kaduna ya ce yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan 800 matsayin kudin fansa kafin su sako daliban 23, Vanguard ta ruwaito.

"Ana tattaunawa, masu garkuwar sun tuntubi wasu iyalan daliban suna neman a biya Naira miliyan 800," a cewar, Georgina Stephen, yar uwan daya daga cikin daliban da aka ace.

DUBA WANNAN: Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

Greenfield University: Masu garkuwa sun nemi Naira miliyan 800 kudin fansar daliban Kaduna
Greenfield University: Masu garkuwa sun nemi Naira miliyan 800 kudin fansar daliban Kaduna. Hoto: @Vangaurdngrnews
Asali: UGC

Ta ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci yan gidansu su biya Naira miliyan 8 kudin fansa kafin su sako yar uwanta da ke tsare a hannunsu.

KU KARANTA: Sheikh MaiAnnabi: Iyalan malamin Kano sun shiga fargaba yayinda wa'adin da masu garkuwa suka basu ya kusa cika

A cewar Georgina, daliban 23 da aka sace sun kunshi mata 14 da kuma maza 6 da kuma ma'aikatan jami'ar.

Ta ce masu garkuwa da mutanen suna azabtar da daliban inda suka ce idan ba a biyan kudin ba, za su halaka dukkan daliban da suka sace.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel