Kwanaki Bayan Gwamna Ya Nada Shi, Alkali Ya Tunbuke Sarki Daga Kan Kujerar Sarauta

Kwanaki Bayan Gwamna Ya Nada Shi, Alkali Ya Tunbuke Sarki Daga Kan Kujerar Sarauta

  • An kai maganar sarautar Masifa-Ile gaban babban kotun jihar Osun, Alkali ya yanke hukunci a karshen makon nan
  • A hukuncin da ya zartar, Mai shari’a Jide Falola ya gargadi Gwamnatin jihar Osun a kan yin abin da ya sabawa doka
  • Jide Falola ya ruguza zaben sabon Sarkin Masifa, hakan na nufin Prince Josiah Adeleke ba zai hau kan gadon sarauta ba

Osun – A makon nan ne wata babban kotun jiha da ke zama a garin Osogbo a jihar Osun, ta rusa nadin sabon Olaaresa na kasar Masifa da aka yi.

Punch ta kawo rahoto a ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba 2022, inda aka ji Alkali ya wargaje nadin da gwamnatin Osun tayi a makon da ya wuce.

A karshen watan Agusta aka sanar da Prince Josiah Adeleke a matsayin sabon Sarkin Masifa. Baya ga shi an amince da nadin wasu Sarakunan.

Kara karanta wannan

An Fara Sauraron Karar da Aka Kai Domin Karbe Takaran PDP Daga Hannun Atiku

Amma da maganar nadin ta je kotu, sai Alkali Jide Falola ya zartar da hukuncin cewa ayi bincike a kan duk wanda yake ikirarin wannan sarauta.

David Tomori sun je kotu

Wani rahoto da Ripples Nigeria ta fitar dazu ya bayyana cewa Pa David Tomori da wasu mutane biyu ne suka shigar da kara a kan Pa Salawu Oyetunji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

David Tomori yaje kotu ne a madadin daukacin gidan sarautar Lateru, yana kalubalantar Prince Josiah Adeleke ya dare gadon sarautar Masifa.

Oyetola
Gwamnan Osun, Gboyega Oyetola Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Baya ga haka, Mai shari’a Jide Falola ya kuma ja kunnen wadanda suke yaudarar gwamnati kan rikicin gadon sarautar, da su guji tsokano fushin kotu.

Yaudarar Gwamna aka yi?

“Ta tabbata cewa an yaudari gwamnatin jihar Osun wajen daukar matakin da ya saba doka. Watakila ba da gan-gan ba ne, domin ba a saba yi ba.

Kara karanta wannan

Barayin Mai: Gwamnati Ta Kawo Hujjar Ba Tsohon Tsageran N/Delta Kwangilar N48bn

Abin da aka sani shi ne Gwamnati tana tabbatar da doka, akwai bukatar a gargadi wadanda watakila su suka sa gwamnati ta dauki matakin nan.
A makonnin nan kotun daukaka kara tayi wa Mai ba gwamna shawara kaca-kaca kan ya yaudare ta wajen hukuncin a kan sarautar Alawo na Awo.”

A karshen zaman kotun, Alkali ya zartar da hukunci cewa har yanzu babu wanda yake kan karagar Masifa-Ile, a kuma bincike mai da’awar sarautar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel