Atiku Butulu Ne, Bai Da Rana: Tinubu Ya Sake Biyowa Ta Kan Abokin Hamayyarsa

Atiku Butulu Ne, Bai Da Rana: Tinubu Ya Sake Biyowa Ta Kan Abokin Hamayyarsa

  • Jam'iyyar APC ta gudanar da uwar yakin neman zaben yau a jihar Legas, mahaifar dan takararta, Bola Tinubu
  • Jihar Legas ta kasance karkashin mulkin jam'iyyar adawa tun daga 1999 har 2015 da Buhari ya hau mulki
  • Sau biyu kenan a jere Tinubu yana tsokano abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar

Legas - Asiwaju Ahmed Bola Ahmed Tinubu, dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya sake dira kan abokin hamayyarsa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar.

Tinubu ya ce Atiku Butulu ne tunda har yake kokarin takara da shi a zaben 2023, rahoton DailyTrust.

Tinubu a wajen taron yakin neman zabensa da ya gudana ranar Asabar, 26 ga Nuwamba a filin Teslim Balogun dake Legas, ya yi kira ga jama'a su yiwa Atiku ritaya da katin zabensu a 2023 saboda ya daina takara.

Atiku Tinubu
Atiku Butulu Ne, Bai Da Rana: Tinubu Ya Sake Biyowa Ta Kan Abokin Hamayyarsa Hoto: Official ABAT
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi alkawarin cewa zai cigaba daga inda shugaba Buhari ya tsaya kuma za'a dama da kowa.

Yace:

"Yayi takara karkashin PDP. Ya yi takara karkashin ACN, mun karbeshi hannu biyu-biyu. Butulu ne. Bai kamata ya sake takara ba. Kuyi amfani da kuri'unku kuyi masa ritaya."

Wai Sau Nawa Atiku Zai Yi Takara Ne? Ku Fada Masa Yaje Ya Huta: Cewar Tinubu

A jiya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya biyo ta kan Alhaji Atiku Abubakar yayinda ya tafi yakin neman zabensa masarautar Gbaramatu dake jihar Delta.

Tinubu ya shawarci Atiku tunda ya dade yana neman wannan mulki kuma har yanzu bai samu ba kawai ya hakura kuma ya janye.

Tinubu ya yiwa Atiku isgili wai shin sau nawa zai yi takara.

Hukumar INEC Ta gindaya sharrudan yakin neman zaben bana

Hukumar gudanar da zaben kasa mai zaman kanta, INEC, ta fitar da jerin sharrudan yakin neman zabe ga jam'iyyun siyasa da yan takaransa.

A takardar mai shafi shida da INEC ta fitar, ta haramta zage-zagen juna da tsokanar fada a wajen kamfe da kuma tallata wani dan takara a Masallatai ko coci.

Hakazalika hukumar ta kara da cewa jami'an tsaro kadai aka hallatawa rike makami wajen taron kamfe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel