'Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dillalin Bindiga Zai Tafi Jihar Zamfara

'Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dillalin Bindiga Zai Tafi Jihar Zamfara

  • Rundunar 'yan sanda sun kama wani kasurgumin dillalin bindigan da ke kai kaya jihar Zamfara, Arewa maso Yammacin Najeriya
  • An kama shi ne a tsakanin birnin tarayya Abuja da Kaduna yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Zamfara
  • Ana yawan samun miyagun 'yan bindiga da dillalai da ke kara yawan makamai a Arewacin Najeriya

Abuja - Rahoton da muke samu ya ce, jami'an ‘yan sanda a jihar Zamfara sun yi nasarar kama wani da ake zargin kasurgumin dan harkallar bindiga ne a ranar Laraba 31 ga watan Agusta a birnin Gusau.

Jaridar Daily Nigerian ta ce, wanda ake zargin sunansa Sa’idu Lawal mai shekaru 41, ya kuma kasance kofur a rundunar sojojin Najeriya.

An kama shi ne a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna lokacin da yake dauke da bindigu biyu da harsasai da kuma mujallu guda takwas.

Kara karanta wannan

An Fara Sauraron Karar da Aka Kai Domin Karbe Takaran PDP Daga Hannun Atiku

Yadda aka kama wani dillalin bindigan Zamfara
'Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dillalin Bindiga Zai Tafi Jihar Zamfara | Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

An ce yana kan hanyarsa ta zuwa Gusau ne domin kai kayayyakin barnar ga abokin harkallarsa da ke can.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya shaida wa manema labarai cewa Lawal kasurgumin mai garkuwa da mutane ne, dan fashi da makami kuma dan harkallar bindiga.

Abubuwan da aka kama a hannunsa

Ya ce an kwace bindigu kirar AK-47 daya da AK-guda daya kana da harsasai 200 masu girman 7.6mm, alburusai 501 masu girman 7.62x51mm da kuma mujallu takwas da babu komai ciki.

Shehu ya shaida cewa, an kama Lawal ne a wata mota kirar Pontiac Vibe mai lambar Legas KRD 686 CY a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna lokacin da yake nufin tafiya Zamfara, rahoton Ripples Nigeria.

A cewar dan sandan:

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: ‘Yan Gari Sun yi Wa Shugaban Karamar Hukumarsu Ruwan Dutse

“Da aka titsiyeshi da tambayoyi, hatsabibin ya amsa cewa ya dauko kayayyakin da yake dauke dasu ne ne daga karamar hukumar Loko ta Jihar Nasarawa zuwa ga wani abokin harkallarsa, Dogo Hamza, a kauyen Bacha dake karamar hukumar Tsafe a Zamfara.
“Ya kuma ambaci cewa, a baya ya taba kai irin wadannan kayayyaki ga sauran abokan harkallarsa a jihohin Kaduna, Katsina, Neja da Kebbi."

Shehu ya kara da cewa ‘yan sanda na ci gaba da bincike kuma za su tabbatara da kamo abokan harkallar Lawal.

'Yan Ta'adda Sun Farmaki Sojojin Najeriya, Sun Kashe 2, Sun Jikkata 4 a Katsina

A wani labarin. yanzu muke samun labarin cewa, wasu tsagerun ‘yan ta’adda sun yi wa motar sulke ta sojin Najeriya kwanton bauna, inda suka hallaka sojoji sojoji biyu tare da raunata wasu hudu a yankin Shimfida dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Jaridar This Day ta ce ta samo daga majiya cewa, an yi wa sojojin kwanton bauna ne da misalin karfe 10 na safe yayin da suke raka wasu jama'a zuwa garin Jibia domin siyo kayan abinci.

Kara karanta wannan

2023: Da Yawa Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Kasa Yashe Najeriya Suke da Buri, Wike

Majiyar ta kuma ce, sojojin da aka kashe na daga cikin dakarun bataliya ta 32 ta sojojin Najeriya da aka tura Shimfida dake fama da barnar 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.