Kotu Ta Yi Fatali Da Umarnin Da AKa Bawa DSS Na Biyan Sunday Igboho N20bn

Kotu Ta Yi Fatali Da Umarnin Da AKa Bawa DSS Na Biyan Sunday Igboho N20bn

  • Kotun daukaka kara da ke zamanta a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo ta soke hukuncin da babban kotu ta yanke na cewa DSS ta biya Sunday Igboho N20bn
  • Mai Shari'a Muslim Hassan na kotun daukaka karar ya ce alkalin babban kotun Mai Shari'a Ladiran Akintola ya yi amfani da ra'ayinsa a maimakon abin doka ta tanada
  • Sunday Igboho ya shigar da kara a babban kotun ne inda ya nemi a tabbatar da cewa samamen da DSS ta kai gidansa haramtacce ne kuma a biya shi diyya

Ibadan - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Ibadan, Jihar Oyo, ta soke hukuncin biyan diyya da aka ce hukumar DSS ta bawa mai rajin kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho.

Kara karanta wannan

Karin bayani a kan Abin da ya Hana Kotu ta Bada Abba Kyari a Damka shi ga Amurka

Igboho
Kotu Ta Soke Hukuncin Biyan Sunday Igboho Diyyar N20bn. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Mai Shari'a Muslim Hassan ne ya soke wannan hukuncin, a zaman kotun na ranar Talata, The Punch ta rahoto.

Kotun ta kuma jigine hukuncin da aka yi na ayyana samamen da DSS ta kai gidan Igboho a matsayin haramtaciyya, tana mai cewa cewa kakabawa DSS biyan diya ba dai-dai bane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke yanke hukunci a daukaka karar da Antoni Janar na kasa, direktan SSS na kasa da Shugaban SSS na jihar Oyo suka yi, Mai Shari'a Hassan ya ce Mai Shari'a Ladiran Akintola, wanda ya yanke hukuncin na ranar 17 ga watan Satumban 2021 bai yi amfani da ka'idojin shari'a na suka cancanta ba.

Ya ce Mai Shari'a Akintola ba zai iya kiyasta asarar da Igboho ya yi ikirarin ya yi ba ta hanyar amfani da matakan da ransa ya raya masa.

Kara karanta wannan

Ta tabbata: Dan a mutun Kwankwaso ya rasa kujerar shugabancin PDP a Kano

Kotun ta kuma soke hukuncin da aka yanke na cewa Hukumar DSS ta biya shi diyyar Naira biliyan 20 saboda samamen, tana mai cewa kudin ya wuce hankali.

Mai shari'a Hassan ya ce babban kotun ta jihar Oyo ta ajiye ainin gaskiya abin da ya faru a gefe guda, ya kara da cewa bai kamata alkalin ya yi amfani da abin da zuciyarsa ta raya masa ba.

Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Tuna farko, rahoton da Guardian ta wallafa ya nuna cewa Hukumar DSS tana farautar dan gwagwarmayar mai neman kafa kasar Yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ruwa a jallo.

Hukumar ta DSS ta sanar da hakan ne a daren ranar Alhamis 1 ga watan Yuli yayin taron manema labarai inda ta tabbatar cewa tawagar jami'an tsaro sun kai samame gidan Igboho da ke Soka a Ibadan, jihar Oyo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel