Hotunan Hatsabiban Yan Bindiga 3 Da Sojoji Suka Kama Da Daya Da Aka Kashe A Kaduna

Hotunan Hatsabiban Yan Bindiga 3 Da Sojoji Suka Kama Da Daya Da Aka Kashe A Kaduna

  • Sojojin Najeriya na 1 Division sun fita sintiri a wasu garuruwan Kaduna takwas inda suka fatattaki yan bindiga
  • Dakarun sojojin sun yi nasarar halaka dan bindiga daya tare da kama wasu uku da ransu bayan tafka gumurzu
  • Sojojin sun kwato bindiga da harsashi da babura sannan sun bukaci al'umma su kai rahoton duk wani da aka gani ya zo asibiti da raunin bindiga

Jihar Kaduna - Dakarun rundunar sojoji na 1 Division sun yi nasarar halaka dan bindiga guda daya tare da kama wasu uku da ake zargi a ranar Litinin.

Sojoji A Kaduna
Hotunan Hatsabiban Yan Bindiga 3 Da Sojoji Suka Kama Da Daya Da Aka Kashe A Kaduna. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Mai magana da yawun rundunar sojoji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da lamarin cikin sanarwar da ya fitar a shafin Twitter na rundunar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan Sanda Sun Cafke Masu Kaiwa 'Yan Bindiga Bayanai, Sun Fadi Irin Barnar da Suke yi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar sanarwar, GOC na 1 Division, Nigerian Army, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ne ya jagoranci tawagar da ta kai samamen tare da hadin gwiwan wasu kwamandoji.

Sojojin Najeriya
Hotunan Hatsabiban Yan Bindiga 3 Da Sojoji Suka Kama Da Daya Da Aka Kashe A Kaduna. Hoto: @HQNigerianArmy.
Asali: Twitter

Sojoji a Kaduna
Hotunan Hatsabiban Yan Bindiga 3 Da Sojoji Suka Kama Da Daya Da Aka Kashe A Kaduna. Hoto: @HQNigerianArmy.
Asali: Twitter

Sojoji A Kaduna
Hotunan Hatsabiban Yan Bindiga 3 Da Sojoji Suka Kama Da Daya Da Aka Kashe A Kaduna. Hoto: @HQNigerianArmy.
Asali: Twitter

Nwachukwu ya ce:

"Dakarun sojoji sun yi nasarar fatattakar yan bindiga a garuruwan Buruku, Udawa, Manini, Birnin Gwari, Doka, Maganda, Kuyello da Dogon Dawa a Jihar Kaduna, yayin wani sintiri da suka fita a ranar Litinin.
"A musayar wutan da aka yi, sojojin sun ci galaba kan yan bindigan, suka halaka daya cikinsu, yayin da aka kama uku da ransu kuma wasu sun tsere da raunin bindiga."

Nwachukwu ya cigaba da cewa:

"Tawagar sojojin sun kuma kwato bindigu AK-47 daya, harsashi mai tsawon 7.62mm da babura 18."

Daga karshe ya yi kira ga al'umma su lura da cibiyoyin lafiya, su kai rahoton duk wani da aka gani ya zo da raunin bindiga yana neman a yi masa magani, su kai rahoto ga hukumomin tsaro da suka dace.

Kara karanta wannan

Hankali ya tashi yayin da 'yan bindiga suka sace wani dan kasar waje, suka kashe soja a Kaduna

An Kama Sojoji 2 Kan Laifin Kashe Babban Malamin Islama, Sheikh Goni Aisami, Tare Da Sace Motarsa A Yobe

A wani rahoton, rundunar yan sandan Najeriya a Yobe ta kama sojoji da ake zargi da hannu a kisar fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Goni Aisami wanda aka kashe ranar Juma'a misalin ƙarfe 9 na dare a hanyarsa ta komawa Gashua daga Kano.

Majiyoyi da dama daga garin sunyi zargin cewa sojojin sun kashe malamin ne bayan ya rage musu hanya daga shingen sojoji a Nguru zuwa Jaji-maji, wani gari da ke karamar hukumar Karasuwa na Jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel