Yanzu-Yanzu: Alkali ya Saka Ranar Shari'ar Abba Kyari, Ya Sanar da Lokacin da Za a Dauka

Yanzu-Yanzu: Alkali ya Saka Ranar Shari'ar Abba Kyari, Ya Sanar da Lokacin da Za a Dauka

  • Babbar kotun tarayya dake Abuja ta saka ranakun 19, 20 da 21 na watan Oktoban 2022 domin sauraron shari'ar Abba Kyari
  • NDLEA ta gurfanar da dakataccen 'dan sandan tare da wasu mutum hudu da take zargi da safarar hodar iblis
  • Kamar yadda mai shari'a Emeka Nwite ya bayyana, ba za a bada belin Kyari da mutum 4 ba don haka a cigaba da adana su a magarkamar Kuje

FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya dake zama a Abuja ta saka ranakun 19, 20 da 21 na watan Oktoban shekarar nan domin shari'ar dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sandan Najeriya, Abba Kyari da wasu mutum hudu.

Mai shari'a Emeka Nwite ya saka ranakun a hukuncin da ya yanke na ranar Talata a babban birnin tarayyar kasar, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kotun Tarayya Ta Sake Daƙile Bukatar Belin Abba Kyari da Wasu Mutum Hudu

Hakazalika, ya yi watsi da bukatar bada belin dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sandan da wasu mutum hudu.

Kyari Abba
Yanzu-Yanzu: Alkali ya Saka Ranar Shari'ar Abba Kyari, Ya Sanar da Lokacin da Za a Dauka. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi ta NDLEA ce ta gurfanar da su kan zargin safarar hodar iblis.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An gurfanar da Kyari tare da wasu dakatattun jami'an 'yan sanda da suma hada da ACP Sunday Ubia, ASP James, Sifeta Sunday Agirigba da Sifeta John Nuhu.

A yayin yanke hukunci kan bukatar belin, Mai shari'a Emeka Nwite yace masu bukatar belin sun gaza samar da gamsasshiyar shaida da zata bada damar a bada belinsu.

Nwite don haka ya tabbatar da hukunacin da aka yanke na ranar 28 ga watan Maris din 2022 yana nan.

A daya bangaren, an bukaci a cigaba da tsare wadanda ake zargin a gidan gyaran halin Kuje dake babban birnin tarayya har zuwa lokacin da za a saurari shari'ar a watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Kotun daukaka kara ta mayarwa wani dan takarar gwamnan PDP tikitinsa

Kotun Tarayya Ta Sake Hana Bayar da Belin Abba Kyari da Wasu Mutum Hudu

A wani labari na daban, babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta ƙi amincewa da ba da Belin dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari, da wasu mutum huɗu.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta gurfanar da Kyari da wasu mutum hudu gaban Kotu ne kan zargin safarar miyagun kwayoyi.

Channels TV ta ruwaito cewa a ranar 7 ga watan Maris, 2022, NDLEA ta fara gurfanar da Abba Kyari (wanda ake tuhuma na farko) da wasu mutum Shida kan zargin harkallar shigo da Hodar Iblis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel